Miƙa makaman ’yan bindigar Katsina ya bar baya da ƙura

A yayin da wasu ke yabo, wasu na ganin miƙa makaman da ’yan bindigar suka yi ba zai yi tasirin a-zo-a-gani ba.

Miƙa makaman ’yan bindigar Katsina ya bar baya da ƙura

Wasu bindigogi da tubabbun ‘yan bindiga suka sallama a Katsina.

A karo na biyu a ƙasa da wata ɗaya ’yan bindiga sun sake miƙa makamansu ga sojoji, a wani ƙoƙari na samar da zaman lafiya a Jihar Katsina.

Aminiya ta ruwaito yadda a ranar 19 ga watan Janairun 2025, ’yan bindiga suka miƙa makamansu da mutanen da ke hannunsu, a wani zaman sulhu da jami’an tsaro suka yi da su a yankin Ƙaramar Hukumar Batsari ta Jihar Katsina.

Sojoji da jami’an hukumar tsaro ta DSS da sarakunan gargajiya da mazauna sun halarci zaman na ranar Lahadi a ƙauyen Kofa da ke kid da garin Batsari.
A wannann karoj manyan ’yan bindiga irin su Umar Black, Abdullahi Lankai da Jijjige da Musa Dan Gandu da Abu Radda, da sauransu, waɗanda d suka adsabi yankunan Batsari da Jibia da Safana, ne suka ajiye makamainsu.

Sani samu rabuwar kai

Ajiye makaman da ’yan ta’addan suka yi ya haifar da rabuwar kai a tsakanin mutane inda wasu ke yabawa tare alaƙanta shi da tsananta ragargazar da sojoji ke wa ’yan ta’adda.

A gefe guda kuma wasu kuma na zargin Gwamnatin Tarayya Nana hannu wajen yin sulhu da ’yan ta’addan ta bayan fage domin a sami zaman lafiya a Jihar.

Al’ummar Batsari sun halarci taron mika malaman inda sun bayyana ra’ayoyi mabanbanta.
Wasu na ganin abin yabo da da ta kamata a ba wa goyon, wasu kuma na ganin sa a matsayin tarin shayi, saboda an mayar da al’ummar da hare-haren suka shafa saniyar ware.

Wani mazaunin yankin ya ce, “Ba a gayyace mu ba amma na je na ga abin da aka yi. Kimanin motoci takwas na APC da hiluxs ɗauke da sojoji da ’yan sanda da jami’an tsaron CWC da ’yan banga.

“Na ga ’yan bindigar sun miƙa wa sojoji bindigogi biyu ƙirar Machine Gun sun neman a basu damar shiga garuruwanmu da kasuwanninu ba tare da wani ƙaido ba.

“Duk da cewa ba duk makamansu suka miƙa ba, amma na yi imani abu mai kyau ne kuma ya kamata a dama da duk hukumomin tsaro,” in ji shi.
Wani ɗan yankin kuma ya ce babu yadda za a yi sulhun ya yi nasara ba tare an sanya mutanen ya yankunan da abin ya shafa ba.
Ya ce, “a na farkon da ka yi, kawai jerin gwanon motocin jami’an tsaro muka gani suna zuwa wurin. Shi ne wasunsu suka je, inda suka ga ’yan bindiga sun mika musu bindigogi biyu. Haka kuma aka yi a na biyun da ka yi jiya.
“Amma ban je na jiyan ba, saboda ina tunanin babu abin da zai tsinana,” in ji shi.

Gwamna Radda ya jaddada matsayinsa

Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, wanda ya ziyarci Batsari ya jaddada matsayinsa cewa gane da sulhu da ’yan bindigar cewa gwamnatinsa ba za ta roƙe su ko ta lallashe su su miƙa makamansu ba.

Ya ce “mun sha faɗa cewa babu ɗan bindigar da za mu je mu roƙe shi don a samu zaman lafiya. Amma idan su da kansu suka zo suka miƙa wuya za mu karɓe su,” in ji a yayin wani gangamin yaƙin nemba Batsari gabanin zaɓen ƙananan hukumomin jihar da za a gudanar ranar Asabar.

Sojoji sun doki ’yan sanda kan kama ‘mai laifi’

Miƙa makaman ’yan bindigar Katsina ya bar baya da ƙura

Fitaccen ɗan siyasa Ahmadu Haruna Zago ya rasu

NAJERIYA A YAU: Kalubalen Da Ke Durƙusar Da Gidajen Rediyo A Arewa