Miji da mata da kwarto sun tare a daki guda
“Watakila mutane su dauka na haukace, amma gaskiyar magana ita ce ina son mijina da kwarton da nake hulda da shi, asalima na kasa tantance wanda na fi so a tsakaninsu”, inji wata mata mai ’ya’ya biyu mai suna Maria Butzki.A watannin baya ne wannan mata ta yi kaura daga gidan mijinta na asali ta […]
“Watakila mutane su dauka na haukace, amma gaskiyar magana ita ce ina son mijina da kwarton da nake hulda da shi, asalima na kasa tantance wanda na fi so a tsakaninsu”, inji wata mata mai ’ya’ya biyu mai suna Maria Butzki.
A watannin baya ne wannan mata ta yi kaura daga gidan mijinta na asali ta koma wajen saurayinta bayan sun samu sabani, amma bayan da suka sasanta ta koma gida sai ta cigaba da ziyartar saurayinta da hakan ta sa take raba musu kwana.
Bayan da mijin nata ya yi kokarin hana ta sai ta nuna masa hakan ba za ta yiwu ba sai dai ya zabi mataki daya, ko dai ya kyale ta ta cigaba da ziyartar saurayinta a duk lokacin da ta ga dama ko kuma ya sake ta. A bangaren maigidanta da yake matukar sonta ya amince da ta cigaba da ziyartar saurayin nata amma dai kada ta yanke shawarar rabuwa da shi (mijin).
Sai dai labarin da jaridar The Mirror ta Landan ta kalato ya nuna da tafiya ta yi nisa ne sai mijin ya fahimci kwarton nasa mai suna Peter Gruman yana da wadansu dabi’u da yake so da hakan ta sa mijin da saurayin suka kulla abuta ta kut-da-kut.
Wannan abuta tasu ta sa matar ba mijin shawara ya amince kwarton ya dawo gidansu don su cigaba da zama maimakon jigilar da take yi a kullum inda tuni mijin ya amince da shawarar matar tasa.
Tuni mijin matar mai suna Paul ya amince da bukatar matar kuma yanzu haka suna zaune a gida daya, inda suke kwana a daki daya.
Yanzu haka Maria ‘yar shekara 33 da mijinta Paul mai shekara 37 da ’ya’yansu biyu Laura ’yar shekara 16 da Amy ’yar shekara 12 tare da kwarto Peter dan shekara 36 suna zaune lafiya a gidansu a yankin Barking da ke Landan ta Gabas