Miji da mata sun zama Farfesa a tare a BUK

Jami’ar Bayero ta Kano (BUK) ta daga darajar wani malaminta tare da matarsa zuwa matsayin farfesa a lokaci guda.

Miji da mata sun zama Farfesa a tare a BUK

Jami’ar Bayero ta Kano (BUK) ta daga darajar wani malaminta tare da matarsa zuwa matsayin farfesa a lokaci guda.

Wata sanarwa da hukumar gudanarwar jami’ar ta fitar a baya-bayan da daga ma’auratan a cikin jerin malaman jami’ar da suka zama ferfesoshi.

Farfesa Suleiman Mainasara Yar’adua da mai ɗakinsa Farfesa Aisha Haruna sun kasance ma’aikatan jami’ar inda suka kwashe shekara 24 suna aiki a bangarori daban-daban.

Farfesa Yar’adua, kwararre ne a fannin Sadarwa da aikin jarida inda ya bayar da gagarumar gudummawa ta hanyar bincike da rubuce-rubuce.

Haka kuma, Farfesa Aisha Haruna, kwararriya ce a fannin Shari’a, wacce ta fi mayar da hankali kan dokokin haƙƙin dan Adam da kuma nazarin jinsi.

Zaman ma’auratan farfesa a lokaci guda na zuwa ne duba da jajircewarsu a harkokin ilimi kamar yadda hukumar gudanarwar jami’ar ta bayyana.