Miji na son rabuwa da matarsa saboda rashin wanka
Miji ya koka cewa ya sha fama da matarsa ta rika wanka kullum amma ta ki.
Wani magidanci a kasar Indiya, ya bayyana aniyarsa ta datse igiyar aurensa da matarsa da suka shekara biyu tare, saboda ba ta yin wanka kullum.
Bayyana aniyar rabuwa da ita ke da wuya, matar mutumin da ke zaune a yankin Uttar Pardesh na Kasar Indiya, ta garzaya wajen kungiyar mata ta ‘Aligarh Women Protection Cell’ don neman a ceto mata aurenta da yake neman girgidewa.
- Haduwar ’yan Kannywood da ’yan BBNaija ya bar baya da kura
- Matsafa sun kwace bindiga daga hannun ’yan sanda a Bayelsa
A kan haka ne kungiyar ta kira ma’auratan da iyayensu don wayar musu da kai game da lamarin domin samar da mafita ga ma’auratan da ke tare da juna tun a 2019, har suna da da daya.
Jaridar News 18, ta rawaito mai sasanci tsakanin ma’auratan, Bobby Bhai, yana ambato yadda magidancin ya koka game da yadda ya dauki tsawon shekaru yan fama da matar tasa saboda ta rika yin wanka a kullum.
“Ya shaida min yadda yake wahala da ita: Ba ta son yin wanka kullum kamar yadda ya fada mana, shi ya sa yake rokon a raba auren nasu,” inji Bobby Bhai.
Sai dai matar ta nuna cewa ba ta shirya rabuwa da mijin nata ba, saboda haka ta sa a roke shi ya yi hakuri.
Amma kuma ba a ji abin da ta ce ba game da matsalarta ta rashin yin wanka.
Masu shiga tsakani sun roki mijin kan ya jingine batun kashe auren, tare da nuna masa cewa matsalar tasu karama ce wadda za a iya shawo kanta.
Kazalika, kungiyar ta ba wa ma’auratan lokaci don su je su tattauna su shawo kan matsalar tare da sulhunta tsakaninsu.