Miji ya ƙona kansa da matarsa a cikin ɗaki

Wani mutum ya sheka lahira bayan da ya banka wa kansa da matarsa wuta saboda saɓanin da suka samu

Miji ya ƙona kansa da matarsa a cikin ɗaki

Wuta
Hoto Daga Premium Times

Wani mutum ya sheka lahira bayan da ya banka wa kansa da matarsa wuta yankin Ijoka da ke Akure, hedikwatar Ondo.

Mutumin ya yi wannan aika-aika bayan wani sabani da suka suka samu da matarsa kan aurensu.

Ma’auratan sun shafe kusan shekara shekara 20 a tare kuma suna sa ’ya’ya biyu kafin faruwar wannan ɗanyen aiki.

Wakilinmu ya gano cewa kafin faruwar lamarin mutumin ya daina zama tare da matar tasa, saboda abin da wasu makusantansu suka kira saɓanin aure.

Wani jami’in tsaro ya ce akwai yiwuwar mutumin ya yanke wannan ɗanyen hukunci ne bayan duk ƙoƙarinsa na sasantawa da matarsa bai yi nasara ba.

Ya bayyana cewa mutumin ya yi mata haka ne bayan da ya yaudare ta cewa ta zo wurinsa ta ɗauki wasu kaya.

“Bayan ta je sai ya nemi su sasanta su ci gaba da zama tare amma ta ƙi.

“Bayan ta yi watsi da tayinsa na sulhu sai ya kulle ɗakin, ya watsa musu fetur ya cimma musu wuta, nan take ta mutu.”

Mai magana da yawun ’yan sanda na Jihar Ondo, Funmilayo Odunlami, ta tabbatar da aukuwar lamarin, amma ta ce an garzaya da matar zuwa asibiti domin kula da lafiyarta, mijin kuma a wurin ya mutu nan take.

A cewarta, “bayan sun samu saɓani daga baya mijin ya kira matar ta je ta karbi kaya, inda bayan zuwanta ya fara barazanar kashe kansa.

“Daga bisani ya rufe dakin, don su mutu tare, inda ya watsa musu fetur ya ƙyasta wuta, shi ya mutu a wurin amma ita an kai ta asibiti.”

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja