Miji ya amince saurayin matarsa ya tare a gidansu

Matata ba ta yi laifi ba. Ina son in ga matata tana nuna abin da take so wa kanta, tana yin duk abin da ta ga dama.

Miji ya amince saurayin matarsa ya tare a gidansu

Rashin kishin wani mutum ya zama abin mamaki bayan ya bayyana cewa, yana zaune lafiya tare da matarsa da suka yi shekara uku da wani saurayinta har ma sun shigo da shi cikin gidansu.

Prince Soy, matashi mai dafa abinci a kasar Japan kuma mai amfani da intanet, wanda ke tallatawa da siyar da abincin gargajiya na kasar na okara granola a intanet, kwanan nan hankali ya koma kansa.

A ranar 8 ga Yuli, ya sanar a shafin sa na sada zumunta na kafar X cewa, matarsa Seira za ta dawo gida bayan ta shafe wata shida tana karatu a kasashen waje kuma za ta dawo tare da sabon saurayinta.

Rubutun da ya wallafa wanda aka yi ta ce-ce-ku-ce a kai ya yi saurin yaɗuwa, inda ya haifar da zazzafar muhawara game da auren Pince Soy da alaƙarta da ɗaya mutumin.

Da alama dai taƙaddamar ba ta damu mijinta na aure ba, wanda a zahiri ya rubuta ziyarar saurayin matarsa ta gajeran bidiyo da samun martani a shafukan sada zumunta da yawa.

“Matata da saurayinta za su zauna tare. Tana karatu a kasar waje kuma tana da sabon saurayi.

“Za ta dawo Japan tare da shi, kuma zai zauna tare da mu, a cewar Prince Soy, wanda ya fada wa mabiyansa a shafin X.

Ya ƙara da cewa ba shi da matsala da tsarin da ba a saba gani ba.

Ya bayyana cewa, Seira ta gaya masa cewa, tana son yin karatu a ƙasar Australia a bara, kuma ya yarda duk da cewa ya yi mamakin shawarar da ta yanke.

Ta tafi a watan Janairu 2024, kuma a watan Mayu, ta furta cewa ta haɗu da wani mutumin Japan wanda daga baya ya zama saurayinta.

Saboda Prince Soy da matarsa a baya sun yanke shawarar kasancewa cikin kyakkyawar dangantaka, ba shi da wata adawa ga sabon saurayinta.

Ya kuma bayyana sakonnin rubutu na abokantaka da ya yi musaya da saurayin matarsa da kuma kyautar Starbucks (ice cream) da ya ba shi don zagayowar ranar haihuwarsa.

“Ban taɓa haduwa da shi ba, don haka ban san abubuwan da yake so ba, kuma na yi tunanin idan na ba shi wani abu mai tsada ba zai samu natsuwa ba, don haka na ba shi wani abu karami mai aminci, kamar tikitin Starbucks,” in ji Prince Soy.

A ranar 12 ga Yuli, Soy ya wallafa bidiyon kansa yana gaisawa da Seira da saurayinta a filin jirgin sama, kuma a cikin makon da ya gabata, ya ci gaba da rubuta tsarin zaman da ba na al’adar aure ba, tare da saurayin, suna tare a gidansu.

Shi da matarsa suna kwanciya a ɗakin kwana, yayin da saurayin nata yana kwana a kan kujera.

Wani lokaci sai matarsa da saurayinta suka sami sabani, sai ya shiga don yin sulhu.

“Na gode masa da gaske lokacin da yake tallafa wa matata yayin da take cikin wahala a kasar waje,” in ji Prince Soy.

“Dole ne ya zama mutum da kowa zai yi sha’awa, ko matata ba za ta faɗa masa ba.”

Ra’ayoyin jama’a a shafukan sada zumunta game da lamarin Prince Soy sun yi ta janwo muhawara, inda wasu suka yaba da niyyarsa ta bijire wa ka’idojin zamantakewa da kuma mutunta yarjejeniyar da aka ƙulla da matarsa game da dangantakarsu da juna, yayin da wasu suka ce ba za su iya fahimtar yadda ya dace da alakar zaman soyayyar mutum uku ba, musamman ganin cewa, bai taba samun wata abokiyar zama ba tun bayan auren Seira.

Dangane da amsar tambayoyi kamar “Me ya sa kake gafarta wa matarka ta yi duk abin da take so?”, sai Prince Soy ya ce, “da farko, kalmar ‘gafara’ ba daidai ba ce.

“Matata ba ta yi laifi ba. Ina son in ga matata tana nuna abin da take so wa kanta, tana yin duk abin da ta ga dama, matar da ba ta nuna abin da take so, ba ta burge ni.”

Prince Soy ya kara da cewa, a koyaushe ya san cewa, sha’awar matarsa ita ce, “samun saurayi,” amma bai taba samun matsala da hakan ba, saboda yana farin ciki matuƙar tana farin ciki.

Ya ce, a wani ɓangare, yana jin tausayin samarin Seira, domin ba za su taɓa samun matsayinsa a cikin zuciyarta ba.

 

An sake zaɓen Obasa Kakakin Majalisar Legas

Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da rabon abincin buɗa-baki

HOTUNA: Tinubu ya karɓi baƙuncin Shugaban Saliyo a Abuja

NLC ta yi fatali da yunƙurin ƙara kuɗin lantarki