Miji ya fasa wa matarsa ido ya karya mata haba
Kotu ta sa a tsare shi a gidan yari bayan ya amsa laifinsa.
Wani magidanci ya fasa wa matarsa ido, ya kuma karya mata haba a garin Girei na Jihar Adamawa.
Aminiya ta gano cewa mutumin ya lakada wa matashiyar matar tasa duka ne har ta kai ga ya fasa idonta na hagu, baya ga karya mata haba da ya yi a lokacin.
- Yadda muka binne mutum 76 a rana guda —Sarkin Musulmi
- Budurwa ta mutu suna tsaka da lalata a cikin mota
Mutumin ya yi wa mai dakin tasa aika-aikan ne saboda wata rashin jituwa da suka samu a tsakaninsu a ranar Alhamis.
Sakamakon haka ne aka gurfanar da magidancin a gaban wata kotun majistare, ana tuhumar shi da yi wa matar tasa munanan raunuka da kuma sauran laifuka, ya kuma amsa cewa ya aikata.
Ana zargin cewa akalla sau bakwai mutumin yana yi wa matar tasa dukan tsiya, saboda sun samu sabani a tsakaninsu, ko da kuwa a gaban ’ya’yansu ne.
Amma a nasa bangaren, magidanci ya shaida wa kotun cewa abin ya faru ne bayan matar tasa ta cakume shi ta al’aurarsa a lokacin da suka samu sabanin a tsakaninsu.
Ya kuma zargi matar tasa da haddasa duk fitintinun da ke faruwa a gidansa, inda ya ce ko a ranar da abin ya faru, bai fara dukan ta ba sai bayan da ta cakume masa al’aura.
Bayan magidancin ya amsa lafinsa, alkalin kotun, Mai Shari’a Abdulrazak Adamu, ya bayar da umarni cewa a tisa keyarsa zuwa Gidan Yari da ke birnin Yola.
Alkalin Kotun ya ce za a ci gaba da tsare magidancin zuwa ranar 22 ga watan Nuwamba, 2021 inda kotun za ta ci gaba da sauraron shari’ar.
Sai dai a lokacin zaman kotun, matar mutumin, wadda suke da ’ya’ya biyar tare ba ta iya yin magana ba saboda karayar da ta samu a habarta da kuma dinki da aka yi mata.