Miji ya datse wa matarsa hannu saboda rashin haihuwa

Magidanci ya fille wa matarsa hannu saboda rahisn haihuwa

Miji ya datse wa matarsa hannu saboda rashin haihuwa

Wani magidanci da ya fille wa matarsa hannu saboda ba ta haihuwa ya gamu da fushin kotu.

An gurfanar da mutumin mai shekara 39 ne a gaban kotun bayan ya yi wa matar tasa aika-aikan inda ake tuhumar sa da yunkurin kashe ta.

Bayan sauraron karar, alkalin kotun, Mai Shari’a  Brenda Bartoo ya yanke wa wanda ake tuhumar hukuncin daurin shekara 30 a gidan yari saboda kama shi da laifin yunkurin aikata kisa.

Mai Shari’a  Brenda Bartoo ya ce hukuncin shi ne abin da ya dace saboda magidancin bai nuna alamar nadama ba kan fille hannun matar tasa da ya yi.

Bayan yanke hukuncin, kotun da ke da ke zamanta a yankin Machakos na kasar Kenya, ta ba wa mutumin ya aikata laifin tun a shekarar 2016 laifin damar daukaka kara cikin kwana 14.

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya