Miji ya gano bidiyon auren matarsa da wani

An kama mutum biyar da suka shiga cikin shari’ar auren na yaudara.

Miji ya gano bidiyon auren matarsa da wani

Hoton bidiyon matar Yin Cheng lokacin da aka wallafa a shafukan sada zumunta

Wani dan kasar China ya yi matukar shiga damuwa bayan da ya binciki manhajar bidiyo a Intanet, inda ya ci karo da hoton bidiyon da aka dauka kwanan nan wanda yake nuna matarsa a wajen bikin daurin aurenta da wani mutum a wani garin da yake kusa da garinsu.

A lokacin da mutumin mai suna Yin Cheng yake da shekara 35 ana daukarsa a matsayin, “saurayi mai shekaru fiye da sa’o’insa” a garinsu na birnin Bayannur da ke Arewacin China a yankin Mongoliya, don haka ba abin mamaki ba ne danginsa sun tursasa shi neman aure.

Amma wannan ba abu ne mai sauki ba a kasar China a wannan zamani, don haka a farkon bana, Yin Cheng ya nemi taimakon wani mai harkar hada aure, wanda ake kira Li, inda shi kuma ya gabatar masa da wata mace mai suna Nana.

Kuma bayan ya yi magana da Nana kan nazarin bidiyon da aka wallafa lokaci kadan, ya neme ta zo garin Bayannur don su ga juna, har ma ya aika mata da kudin China Yuan 1,000 (kimanin Naira dubu 63 da 530, a matsayin toshi ba tare da sanin cewa ya fada a hannu batagari ba.

Lokacin da mahaifin Yin Cheng ya hadu da Nana a karon farko, ya nuna fatarsa na haduwa da iyayenta, amma mai daidaita auren ya hanzarta shiga tsakaninsu inda ya shaida musu cewa ana gina wata gada a kauyen su matar, kuma danginta suna cikin yin wani aiki.

Kuma ya ce kamfanin gine-ginen yana biyan iyalai ne gwargwadon yawan mambobinsu, don haka Nana za ta yi asara idan ta yi aure, kafin a sanya hannu a kan yarjejeniyar diyyar.

Iyalin Yin, sun amince su yi bikin aure na gargajiya kawai, kuma su hada gwiwa da jami’an kungiya a yayin da aka kammala yarjejeniyar biyan diyyar.

Cheng da Nana sun yi aure a watan Janairu, kuma matar ta samu sadakin ya kai Yuan dubu 148 (kimanin Naira miliyan 9 da dubu 402 da 524.) da kuma wasu gwalagwalan ado da sauran kyaututtukan aure.

Kwana uku kacal da yin auren, sai Nana ta fada wa angonta cewa, dole ne ta koma gida don zama tare da iyalinta.

Kuma ta sake dawowa gidansa bayan kusan mako daya, amma bayan kwana biyu, sai ta ce, za ta koma gida don taimaka wa mahaifiyarta.

Abubuwa sun ci gaba a haka na wani dan lokaci, amma Yin Cheng bai yi zargin komai ba, domin yana ganin matarsa tana kewar gida ne kawai kuma tana da kusanci da danginta.

Daga baya angon ya fara jin alamar akwai wani abu, zuwa wani lokacin matarsa ta daina amsa kiran wayarsa kuma tana daukar lokaci mai yawa fiye da yadda take yi a gida.

Cheng yana bincike a manhajar bidiyo – wanda yake ganin ya fi masa a kafar sada zumunta ta Tik Tok mai suna manhajar Kuaishou – sai ya ci karo da wani gajeren bikin aure daga garin Didiaozhao.

Amaryar ta yi kama da matarsa, kuma bayan ya sake kallon bidiyon sai ya hakikance cewa ita ce.

Nana ba ta amsa kiran wayarsa, don haka ya ziyarci garin Didiaozhao don fuskantar mutumin da matarsa ta aura kuma ya kai ga karshen abubuwan da suke faruwa.

Bayan ya gama binciko wanda yake neman maye gurbinsa, Yin ya tabbatar da cewa matar da take cikin bidiyon hakika Nana ce, don haka sai ya tuntubi ’yan sanda game da lamarin.

Bincike na gaba ya gano cewa Nana da Li mai dalilin aure suna daga cikin manyan ’yan damfara wadanda suke yin amfani da irin damar wajen yaudarar maza masu neman aure.

An gano cewa sun kware wajen shawo kan wadanda suke neman aure domin su yarda su gudanar da bikin aure na gargajiya kuma su biya sadaki, yayin da suke daga sanya hannu kan takardun aure na hukuma.

A karshe ’yan sanda sun kama mutum biyar da suka shiga cikin shari’o’in yaudarar aure har guda 19, kuma suka haifar da asarar kusan Yuan miliyan 2 (kimanin Naira miliyan 129 da dubu 54.

Tsohon Kwamishinan Kano ya sauya sheƙa daga NNPP zuwa APC

Amurka za ta dawo wa Najeriya N80bn da ta ƙwato daga Diezani

Yadda gwamnati ta yi sulhu da ’yan bindigar Kaduna

‘Da kuɗin yankan farce na je Hajji’