Miji ya karya ƙafa da hannun matarsa saboda fita ba da izininsa ba a Sakkwato

Ana zargin cewa wani magidanci a ƙauyen Durbawa da ke Ƙaramar Hukumar Kware ta Jihar Sakkwato ya karya ƙafa da hannun matarsa saboda ta je asibiti ba da izininsa ba. Da take bayanin yadda lamarin ya faru Malama Halimatu Sadiya wadda take kwance a asibitin kashi da ke garin Wamakko, ta ce mijinta ya karya […]

Miji ya karya ƙafa da hannun matarsa saboda fita ba da izininsa ba a Sakkwato

Ana zargin cewa wani magidanci a ƙauyen Durbawa da ke Ƙaramar Hukumar Kware ta Jihar Sakkwato ya karya ƙafa da hannun matarsa saboda ta je asibiti ba da izininsa ba.

Da take bayanin yadda lamarin ya faru Malama Halimatu Sadiya wadda take kwance a asibitin kashi da ke garin Wamakko, ta ce mijinta ya karya mata ƙafa da hannunta na dama saboda ya ga magani a tare da ita bayan ta dawo duban mahaifiyarta da ke jinya.

“Kusan wata huɗu a yanzu ina fama da rashin lafiya, ya sani (mijinta) har ma’aikacin kiyon lafiya ya kira ya sanya min ruwa amma ciwon sai ƙaruwa yake yi.

“Na roƙe shi ya barni na je asibiti a duba ni amma bai aminta ba, har wani ɗan uwana ya so ya kai ni asibiti da kuɗinsa amma mijina ya ƙi yarda.

“A lokacin da na je duba mahaifiyata da ba ta da lafiya, a nan ne na tambayi shawarar ma’aikacin lafiyar da yake dubata, sai ya ba ni wasu magunguna na yi amfani da su.

“Bayan na dawo gida ne ya ga maganin daga nan ya fara faɗa cewa na tafi asibiti ba da izininsa ba.

“Na faɗa masa cewa ba haka ba ne wanda yake duba mamata ne ya ba ni su.

“Ya nuna shi ba zai aminta ba sai na kai shi wurin wanda ya ba da maganin, na yarda zan kai shi, a lokacin da nake sanya tufafi a ɗakina sai ya shigo ya rufe ƙofa ya fara dukana da sanda sai da ta ƙare.

“A lokacin da ya fahimci ya karya min ƙafa da hannu sai ya dakata ya fara kuka yana roƙon kar na faɗa wa kowa abin da ya faru tsakaninmu ko da wani ya tambaye ni na ce ɗan acaba ne ya kayar da ni a babur.

Bayanai sun ce mutumin ya aminta da laifinsa da ya alaƙanta da sharrin Sheɗan.

Sai dai ya dage kan cewa matarsa ta je asibiti ba da izininsa ba duk da ƙoƙarin da yake yi mata da danginta duk lokacin da suke fama da rashin lafiya.

“Bayan ta dawo wurin dubiyar mahaifiyarta da ba ta da lafiya, na ga wani ƙulli a cikin bokiti da ta zo da shi na so nasan ko mene ne amma ta ƙi barin na sani.

“Na matsa sai na san ko mene ne, na ƙwace bokitin a lokacin da take ƙoƙarin gudu da shi, da na bincika sai na ga katin asibiti da da magani da butar ƙarfe.

“Sai na tambaye ta ya za ki je asibiti ba ki sanar da ni ba, tun da ta san a koyaushe ina kula da rashin lafiyarta kuma ko a a satin da ya gabata sai da na kawo mata ma’aikacin kiyon lafiya ya duba ta,” a cewarsa.

Mutumin ya musanta ta dukan matarsa da sanda, inda ya ce a lokacin da take ƙoƙarin karɓar bokitin a hunnunsa ne ta faɗi ta samu rauni a hannu da kafarta.

“Bayan ta samu matsala a kafa da hannu na kira mai ɗori ya gyara, sannan ɗan uwanta ya kira wani ya gyara, shi ma sai da na biya dubu 50, sannan ya ƙara kawo wani shi ma sai da na biya dubu 25 kuɗin magani.

“Ni ne shugaban kungiyar banga na yankinmu kuma ni manomi ni ɗan ƙaramin abin da nake da shi nake kula da ita tare da macen da ke jinyarta,” a cewarsa.

Mijin ya yi da ya sanin abin da ya faru na sanadiyar samun raunin da matarsa ta yi yana mai cewa zai ɗauki ƙaddarar abin da hakan zai haifar.

“Amma don Allah matata ka da bar ni don ina sonta sosai kuma ni ma na san tana so na, ku ba ta hankuri kar ta bar ni.”

Dangane da dalilin da ba ya son barin matarsa ta je asibiti, ya ce “saboda ba wani asibiti mai aiki a yankinmu.”

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan Sakkwato, ASP Ahmad Rufa’i ya ce har yanzu maganar ba ta kawo saman teburinsa ba.

Sai dai ana rade-raden an kama mijin kuma har miƙa shi ga hukumar ’yan sandan Sakkwato.