Miji ya kashe matarsa a Jigawa
Magidancin ya tare matar a daji sannan ya daba mata wuka a ciki.
Wani magidanci mai shekara 35 a duniya ya fada komar ’yan sanda kan zargin hallaka matarsa a Karamar Hukumar Babura ta Jihar Jigawa.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa, ASP Lawan Shiisu, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar a Dutse a ranar Laraba.
- An kai hari gonar Obasanjo an yi gakuwa da ma’aikata
- Majalisar Kano na neman a kafa ’yan sandan jihohi
Shiisu, ya ce an shigar da rahoton cewar magidancin ya kashe matar tasa ce a ranar 2 ga watan Satumba, a cikin daji.
Ya ce ’yan sanda sun ziyarci wurin da aka yi kisan don yin bincike tare da dauke gawar matar zuwa babban asibitin garin Babura, inda likita ya tabbatar da rasuwarta.
Kazalika, ya ce marigayiyar an tabbatar da samun yankan adda a gefen cikinta na hagu.
Sannan ya ce an mika gawar matar ga ’yan uwanta don yi mata sutura kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.
Shiisu ya kara da cewa an mika wanda ake zargin ga sashen binciken manyan laifuka da ke Dutse, babban birnin Jihar don gudanar da bincike mai zurfi.
Kakakin ’yan sandan, ya tabbatar da cewa ’yan sandan jihar za su ci gaba da kare rayuka da dukiyoyi al’ummar jihar.