Miji ya kashe matarsa kan N1,000 a Adamawa

Daga ta tambaye shi kudin da ta ba shi aro ya aika ta lahira.

Miji ya kashe matarsa kan N1,000 a Adamawa

Wani magidanci ya shiga hannun hukuma bayan ya kashe matarsa a kan kudin da ta ba shi rance.

Mutumin mai shekara 41 ya lakada wa matar tasa duka har sai da ta bakunci lahira ne bayan ta nemi ya biya ta N1,000 da ta ara masa.

Majiyoyi a unguwar Jada a Karmar Hukumar Ganye ta Jihar Jihar Adawama sun ce mutumin ya sa karfin tuwo ya buga kan matar a bango, nan take ta fadi magashiyyan.

Ganau sun ce an dauki matar ranga-ranga zuwa asibiti amma likitoci suka tabbatar cewa rai ya riga ya yi halinsa.

Ana cikin haka ne matanen unguwa suka yi wa mutumin kofar rago suka tsere shi, su kuma dangin matar suka kai kara caji ofis, ’yan sanda suka je suka cukwikwiye mutumin wanda ma’aikacin gwamnati ne.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Aliyu Adamu Alhaji, ya yaba wa mutanen unguwar da suka tsare mutumin suka hana shi tserewa suka kuma sanar da ’yan sanda.

Kakakin ’yan sandan Jihar Adamwa, DSP Suleiman Nguroje, ya ce Kamishinan ya ba da umarnin a gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da ganin mutumin ya girbi abin da ya shuka.

Amurka za ta dawo wa Najeriya N80bn da ta ƙwato daga Diezani

Yadda gwamnati ta yi sulhu da ’yan bindigar Kaduna

‘Da kuɗin yankan farce na je Hajji’

Zambar Intanet: EFCC ta kama ’yan China 4 da wasu 101 a Abuja