Miji ya kashe matarsa saboda abincin buɗa-baki a Bauchi

’Yan sanda sun kama mijin, sun ɗauko bulalar da aka yi amfani da ita domin gudanar da bincike.

Miji ya kashe matarsa saboda abincin buɗa-baki a Bauchi

’Yan sanda sun cafke wani magidanci mai shekaru 50, Alhaji Nuru Isah kan zargin lakaɗa wa matarsa dukan da ya yi ajalinta a dalilin abincin buɗa-baki.

Bayanai sun ce taƙaddamar wadda aka soma gudanar da bincike a kanta ta auku ne a ranar Asabar a yankin Fadaman Mada da ke Jihar Bauchi.

Kakakin rundunar, CSP Ahmed Mohammed Wakil ya ce, “saɓani ne ya kaure tsakanin wani mai suna Nuru Isah mai shekara 50 da matarsa ta biyu, Wasila Abdullahi kan tsarin abinci da kayan buɗa-baki na gidan.”

’Yan sanda sun ce bincike farko na nuna cewa mijin ya yi amfani da bulala wajen bugun matar mai shekaru 24, “inda ta yanke jiki ta faɗi, da aka kai ta asibitin koyarwa na jami’ar Tafawa Ɓalewa ne likitoci suka tabbatar da rasuwarta.”

Sanarwar ta ƙara da cewa ’yan sanda sun kama mijin, sun ɗauko bulalar da aka yi amfani da ita, sannan kuma za a yi binciken ƙwaƙwaf a kan gawar.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Auwal Musa Muhammad, ya bayyana cewa za a gudanar da bincike domin tabbatar da adalci a lamarin.