Miji ya kashe matarsa saboda koko a Neja

Ya lakada mata duka, ta fadi magashiyyan nan take rai ya yi halinsa.

Miji ya kashe matarsa saboda koko a Neja

Wani magidanci ya kashe matarsa saboda sabanin da suka samu a kan koko a Jihar Neja.

Majiyoyi daga kauyen Kadaura na Karamar Hukumar Rafi a Jihar sun ce matar ta bakunci lahira ne bayan mijin nata mai shekara 20 ya lakada mata duka, ta yanke jiki ta fadi magashiyyan nan take rai ya yi halinsa.

Kakakin ’yan sanda a Jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya ce, “Wanda ake zargin ya amsa cewa ya yi matar tasa duka saboda dan sabanin da suka samu a kan koko.

“Nan take ta fadi magashiyyan, aka dauke ta ranga-ranga zuwa Babban Asibitin da ke garin Wushishi inda likitoci suka tabbatar cewa rai ya yi halinsa.”

Kakakin ’yan sandan ya kuma tabbatar wa Aminiya cewa ’yan sanda na tsare da matashin magidancin a Babban Ofishinsu da ke garin Kagara, suna masa tambayoyi.

“An riga an fara bincike kuma da zarar an kammala za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu,” inji DSP Wasiu Abiodun.

Labarin kisan na zuwa ne mako guda bayan wani makamancinsa inda ake zargin wata matar aure da lakada wa kishiyarta duka da muciya har ta mutu, sannan ta kona gawarta.

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya