Miji ya saki matarsa saboda zanen Tinubu

Matar ta ce ba ta nadamar sakin ta da ya yi saboda zanen ‘tattoo’ din Tinubu a gadon bayanta

Miji ya saki matarsa saboda zanen Tinubu

Zanen hoton Tinubu da ranar haihuwarsa a gadon bayan matar.

Wata mata ta ce mijinta ya fatattake ta daga gidansa saboda zanen ‘tattoo’ din Jagoran Jam’iyyar APC na Kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da ta yi a gadon bayanta.

Ta ce zanen tattoo din da mjinta ya yi ‘waje-rod’ da ita a kan shi, ta yi shi ne domin ta nuna godiyarta ga Tinubu, wanda ta ce uban gidanta ne.

“Mijina ya kore ni daga gidansa, saboda zanen tattoo da na yi [a gadon bayana], ga shi ba ni da inda zan je. A taimaka mini,” inji ta.

Ta kara bayyanawa a daya daga cikin sakonnnin da ta wallafa shafinta na Twitter cewa iyalanta sun yi ta zagin ta har ta kai ga sun kaurace mata saboda zanen.

“Iyalaina, musamman mahaifin dana ya rabu da ni tare da zagi na saboda zanen tattoo din, wanda kuma na yi ne domin in nuna godiyata ga uban gidana. Abin taikaici,” kamar ya dda ta bayyana.

Sai dai, a wani sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter (@AyokunmiBabato1) a ranar Asabar, matar ta ce ba ta da-na sanin korar ta da mijin nata ya yi mata.

“Ba na jin takaicin ko kadan saboda na yaba wa uban gidana,” amma ta kara da cewa, “Babana ka taimaa mini,” wanda ake ganin Tinubu take nufi.

Kallai bidiyon matar da ta zana hoton Tinubu a gadon bayanta

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya