Miji ya sassari matarsa da adda saboda budurwarsa
Wani magidanci mai suna Chima da budurwarsa sun tsere bayan da rikici ya barke ya kai ga sun sassari matarsa da adda a yankin Omerelu a karamar Hukumar Ikwerre da ke Jihar Ribas. Rahotanni sun ce rikicin ya samo asali ne lokacin da matar mutumin mai suna Nwakaego ta hangi mijin ya shiga gidansu da budurwar […]
Wani magidanci mai suna Chima da budurwarsa sun tsere bayan da rikici ya barke ya kai ga sun sassari matarsa da adda a yankin Omerelu a karamar Hukumar Ikwerre da ke Jihar Ribas.
Rahotanni sun ce rikicin ya samo asali ne lokacin da matar mutumin mai suna Nwakaego ta hangi mijin ya shiga gidansu da budurwar tasa a ranar Litinin. Mijin ya tsere bayan aika-aikar da suka tafka, lokacin da ya ga jini ya kece wa matarsa.
- Yadda ambaliya ta ki ci ta ki cinyewa a shataletalen Baban Gwari a Kano
- Mai shekara 27 ya kasa samun aiki saboda yana da fuskar yara
Dan uwan matar mai suna Anayo Warisi, ya shaida wa manema labarai a Fatakwal cewa surukinsa da budurwarsa sun sassari ’yar uwarsa hari da adda inda ta samu munanan raunuka a kafarta, kuma an kai ta asibiti.
Ya ce, “A safiyar yau (Litinin) mijin ’yar uwata ya kawo wata mace gidansu. Dalilin haka ta tambaye shi. Shi ne shi da budurwar tasa suka fara dukanta.
“Sun yanke ta da adda a wurare da dama a jikinta, amma kafarta ta fi samun mummunan rauni. ’Yan uwanmu ne suka kai ta asibiti a Elele, kuma asibitin sun ki karbarta saboda raunin da ke jikinta ya yi yawa.
“Daga baya ne suka kai ta Asibitin Koyarwa na Jami’ar Fatakwal (UPTH), inda ake kula da ita yanzu.
“Muna so a kama mijinta saboda wannan shirin kisa ne. Idan muka yi shiru babu wanda zai san abin da ya faru. Muna bukatar a yi adalci,” inji shi.
Wata kungiyar Kare Hakkin dan Adam da Zabe a jihar, ta yi kiran a gudanar da cikakken bincike a kan lamarin.
Sakatariyar kungiyar, Gladys Oyenmwen, ta ce duk wanda aka samu da laifi a hukunta shi.
Ta ce “Bai kamata a bar kowane irin rikici da ke faruwa a gidajen aure ba, kowa aka samu da laifi yana da kyau ya fuskanci hukunci.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Ribas, Grace Iringe Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce yanzu haka sun kama budurwar.
“An kama budurwar kuma an mika ta ga Sashen Binciken Manyan Laifuffuka don zurfafa bincike,” inji ta.
Ta ce ana kokarin gano mijin matar don gurfanar da shi a gaban shari’a.