Mijin Sarauniyar Ingila, Yarima Philip ya rasu

Yarima Philip ya rasu yana shekara 99 a duniya

Mijin Sarauniyar Ingila, Yarima Philip ya rasu

Marigayi Yarima Philip. (Adrian Dennis/Pool via AP)

Yarima Philip, mijin Sarauniyar Elizabeth II ta Ingila ya rasu a Fadar  Buckingham bayan shekara 99 a duniya.

Fadar Buckingham ta tabbara da rasuwar Yarima Philip, wanda shi ne Magajin Garin Edinburgh a ranar Juma’a 9 ga Afrilu, 2021.

“Cikin alhini da kaduwa, Mai Alhfarma Sarauniya na sanar da rasuwar mijinta, Mai Martaba Yarima Philip, Duke na Edinburgh lami lafiya…” inji sanarwar da ta ce nan gaba za a bayyana tsare-tsaren jana’iza da zaman makokin mamacin.

A watan Fabrairu aka fara kwantar da Yarima Philip a asibiti a birnin London sakamakon ciwon zuciya, kafin daga bisani a sallame shi a sakiyar watan Maris, bayan an yi masa tiyata.

A ranar 10 ga watan Yuni, 1921 ne aka haifi Yarima Philip a Tsibirin Corfu na kasar Girka.

Iyayensa su ne Yarima Andrew na Girka da Denmark —dan Sarki George I— da kuma Gimbiya Alice, ’yar Lord Louis Mountbatten.

A shekarar 1947 Yarima Phikip ya auri Gimbiya Izabel, shekara biyar kafin ta zama Sarauniyar Ingila.

Ma’auratan, su ne suka fi dadewa a kan karagar mulki a tarihin Masarautar. Allah Ya azurta su da ’ya’ya hudu da jikoki takwas da tattaba kunne 10.