‘Mijina ya gudu bayan yunkurin tsafi da ni da ‘ya’yanmu hudu’
Wata matar aure mai suna Abidat Ademola ta roki kotu ta raba aurenta na shekara 12 da mijinta mai suna Isa Ademola bisa zargin yunkurin tsafi don samun kudi dare daya da ya so yi da sassan jikinta da ’ya’yansu hudu in da ya samu nasarar kashe su. Abidat ta shaida wa Kotun Gargajiya ta […]
Wata matar aure mai suna Abidat Ademola ta roki kotu ta raba aurenta na shekara 12 da mijinta mai suna Isa Ademola bisa zargin yunkurin tsafi don samun kudi dare daya da ya so yi da sassan jikinta da ’ya’yansu hudu in da ya samu nasarar kashe su.
Abidat ta shaida wa Kotun Gargajiya ta Oja Oba/Mapo da ke Ibadan cewa, asirin mijinta ya tonu ne a lokacin da ya fara yin wasu abubuwan mamaki da bai saba yi a shekara 12 da suke zaune a matsayin miji da mata ba.
Ta ce, hakan ne ya sa ya kasa amsa tambayoyin da ta yi masa kan abubuwan da suka shafi tsafin da yake yi a cikin gidansu. “Maimakon amsa tambayoyina sai mijina ya tattara nasa-ya-nasa ya fice daga gidan ba tare da sanin inda ya koma da zama ba. Hakan ya biyo bayan kararsa da na kai zuwa gidan iyayensa ne,” inji ta.
Abidat, wacce ke kuka lokacin da take bayanin gallazawar da take zargin mijinta da yi mata ita da ’ya’yansu hudu musamman rashin abinci da bukatun yau da gobe, ta roki kotun ta raba aurensu. “Kuma ina rokon a kyale mini yaran in ci gaba da kula da su. Kuma ina rokon kotu ta tilasta wa mijina biyan kudin abincin yaran kuma a hana shi zuwa gidan iyayena da wurin aikina yana ci min mutunci a gaban jama’a,” inji ta.
Mijin wannan mata bai bayyana a gaban kotun ba duk da sammacin da aka aika masa kafin ranar Juma’a da ta gabata da aka saurari karar.
Da yake yanke hukunci Alkalin Kotun Cif Ademola Odunade, ya raba auren tare da amince wa Abidat ta ci gaba da rike ’ya’yansu hudu, kuma kotun ta umarci Isa Ademola ya rika aikewa da Naira dubu 20 a kowane wata ga tsohuwar matarsa domin daukar dawainiyar ’ya’yansu. Kotun ta ce, zai rika aikawa da kudin ne ta hannun kotun kuma ya gargade shi da kada ya sake zuwa gidan matar ko wurin aikinta.