Mijina ya sake ni don na haifi ’yan uku – Binta Sa’idu

Murnar wata maijego da ta haifi ‘yan uku mai suna Binta Sa’idu, da ke zaune a Unguwar Gobirawa a yankin karamar Hukumar Dala, ta koma ciki sakamakon sakinta da mijinta ya yi a kan haihuwar da ta yi.Duk da cewa an dauki kimanin kawanaki 70 da haihuwar  ‘ya ukun, da suka hada da maza biyu […]

Mijina ya sake ni don na haifi ’yan uku – Binta Sa’idu

Murnar wata maijego da ta haifi ‘yan uku mai suna Binta Sa’idu, da ke zaune a Unguwar Gobirawa a yankin karamar Hukumar Dala, ta koma ciki sakamakon sakinta da mijinta ya yi a kan haihuwar da ta yi.
Duk da cewa an dauki kimanin kawanaki 70 da haihuwar  ‘ya ukun, da suka hada da maza biyu da mace daya, amma har yanzu daya daga cikin ‘ya’yan ba a samu damar yanka masa abin akika ba, kasancewar mahaifin nasu rago da tunkiya kawai ya bayar, kamar yadda maijegon ta shaida wa Aminiya.
Aminiya ta rawaito cewa, rigima a tsakanin ma’auratan wadanda ba su wuce shekara daya da aure ba ta taso ne  un daga lokacin da maijin nata mai suna Sulaiman Musa ya fahimci tana da juna biyu makonni biyu bayan aurensu, inda ya nuna mata cewa ta yi saurin daukar ciki tun ba su kai ga kammala cin amarci ba. Daga baya kuma sai ya dauki matakin zubar da cikin, inda ya rika kawo mata magunguna tare da  umurtarta da ta je asibiti a yi mata wata allura, lamarin da ita kuma ta kekashe kasa ta ki amincewa da shi.
Rigima ta kara tsananta ne a lokacin da kwanakin cikin ya tura, inda suka je asibiti aka yi mata hoto aka tabbatar mata da cewa ‘yan uku za ta haifa. A nan fa maigidan ya yi tsalle ya ce bai san wannan zancen ba, domin a cewarsa, samun ‘ya’ya uku a lokacin guda sun yi masa yawa.
A cewar Maijegon, “Tun daga wannan lokacin da aka yi min hoto ya ji cewa ‘ya’ya uku zan haifa sai ya ce shi gaskiya ‘ya’ya uku matsala ne, domin ba zai iya daukar nauyinsu ba. Daga nan sai ya dauke kafarsa ya daina zuwa gidana, sai dai idan ya ga dama. Haka muka zauna har cikin ya kai wata bakwai, inda a karshe ya sake ni. Kasancewar ina dauke da cikinsa sai na nemi ya rika ba ni kudin abinci, wata rana ya aiko mini, wata rana kuma sai dai makwabta su taimaka mini. Hakan ya sa na kai shi kara kotu, amma dai ba ta canza zani ba. To daga nan ne sai na shiga sana’ar wanki don in samu abin da zan ci har Allah Ya sauke ni lafiya. “ inji ta.
Binta ta kara da cewa, bayan ta haihu babu abin da uban ‘ya’yan ya yi mata na al’adar haihuwa, sai dai dan abin da ba a rasa ba. “ bayan na haihu babu abin da ya kawo mini, ko wando bai kawo wa yaran ba, sai jama’ar Annabi ne suka rika taimaka mini da kayan jarirai da kuma kayan abinci. “
Maijegon wacce ta ce ba ta da wanda zai dauki nauyinta a halin yanzu kasancewarta marainiya, ta bayyana cewa babu abin da take so a yanzu illa samun abin da za ta rika ciyar da jariran, kasancewar nonon da take ba su ba ya isarsu. “Abin da yake damuna a yanzu shi ne samun abincin da zan rika ba yaran, kasancewar nono ba ya isarsu, gashi kuma babansu ya ki saya musu madara, tun farkon da aka haife su ya da saya musu gwangwani uku, bai sake saya ba. A lokuta da dama sai dai su yi ta kukan yunwa. A yanzu haka madarar da wani makwabcinmu ya saya wa yaran ta kare.’’ Inji ta.
Binta ta kara da cewa, a yanzu haka kudin hayar gidan da suke zaune ya kare, har masu gidan suna kokarin korarta, domin maigidanta ya ce ba zai sake biya mata kudin haya ba.
Duk kokarin Aminiya don jin ta bakin angon karnin, wato mahaifin ‘yan uku, Malam Sulaiman Musa, wanda kuma ma’aikaci ne a asibitin kula da masu cututtukan da suka shafi kwakwalwa na Dawanau da ke Kano, amma abin ya ci tura, domin kuwa cewa ya yi ba zai yi magana da ‘yan jarida a kan batun ba, tunda sun riga sun rabu da matar magana ta kare.
Abubakar Mati Salihu shi ne Mataimakin Kwamandan Hisbah na karamar Hukumar Dala, ya bayyana wa Aminiya cewa, sun nemi uban ‘ya’yan ya mayar da matarsa, amma kememe ya ki amincewa. “Mun yi kokarin mu yi musu sulhu a mayar da auren, amma mijin ya ki yarda, domin a cewarsa, ba ta da kirki, domin tunda suka yi aure ba su zauna lafiya ba. Sai dai ya tabbatar da cewa ‘ya’yansa ne kuma zai karbe su, amma ba zai mayar da uwarsu ba.” inji shi.
A cewar shugaban Hisbar, hukumarsu tasu ta tilasta wa uban ‘ya’yan biyan Naira dubu 11 da 500 duk wata domin uwar ‘ya’yan ta samu abin da za ta rika ciyar da su. “Mun tilasta masa cewa dole ya rika biyan ta Naira dubu 11 da 500 a matsayin kudin abincinta da na yaran, kasancewar har yanzu tana da hakki a kansa. A yanzu haka ma ya bayar da Naira dubu hudu, inda ya yi alkawarin zai ciko ragowar zuwa karshen wata.”
Binciken Aminiya ya gano cewa a yanzu haka Allah Ya sake azurta wannan mutumin, wato mahaifin ‘yan uku da samun wadansu tagwayen da uwargidansa ta haifa masa, lamarin da ya sa ya zama uban ‘ya’ya biyar ken an a cikin shekara guda.

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi

NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi tan 3.9 da kama mutum 599

An kashe ’yan gudun hijira uku a Sakkwato