Mika makamai ga jami’an tsaron sa kai zai haifar da tashe-tashen hankula
Shawara da Shugaban Hukumar Kula da Ayyukan ’Yan sanda, Mista Mike Okiro, kuma tsohon sufeto Janar na ’yan sanda, ya bayar cewa a mika ga kungiyar matasa masu sa kai a harkar tsaro (Cibilian JTF), wajen shawo kan rikicin boko haram, ya kamata a yi takatsantsan a kanta. Wadannan matasa sun fito ne kawai, kuma […]
Shawara da Shugaban Hukumar Kula da Ayyukan ’Yan sanda, Mista Mike Okiro, kuma tsohon sufeto Janar na ’yan sanda, ya bayar cewa a mika ga kungiyar matasa masu sa kai a harkar tsaro (Cibilian JTF), wajen shawo kan rikicin boko haram, ya kamata a yi takatsantsan a kanta. Wadannan matasa sun fito ne kawai, kuma sun samu karbuwa a wajen jami’an tsaro, don tabbatar da zaman lafiya a Jihar Barno, inda rikicin Boko Haram ya yi kamari. Wajen yaye jami’an ’yan sanda wadanda suka halarci kwas din mataimakin sufuritanda (ASPs) da Insufeto a makaranta Horar da Jami’an ’yan sanda ta Wudil da ke Kano, Mista Mike Okiro ya jadadda bukatar dora wadannan amtasa a kan tafarkimn aikin tsaro irin na ’yan sanda, don bai wa rayuka da muhalli kariya. Wannan kira da ya yi ya zo daidai lokacin da wadannan matasa ke kokarin ganin Gwamnatin Jihar Barno ta fara biyansu alawu-alawus a kowane wata.
Wannan kungiyar tsaro a sa kai, wadda ake yi wa lakabi da Cibilian JTF ta bayyana a jihohi uku na Arewa maso Gabas, wadanda suka hada da Barno da Yobe da Adamawa, wadanda aka kakaba musu dokar ta baci, saboda matsalar Boko Haram. Wadannan matasa sun zagaya unguwanni a cikin birnin Maiduguri, inda suke zakulo wadanda suka tabbatar ’yan Boko Haram ne, sannan su mika su ga sojoji na jami’an tsaro JTF. Bisa la’akari da masaniyar da suke da ita game da irin wadannan mutane, an amince da wadannan matasa, an kuma samu kwarin gwiwa kan yadda suke gudanar da ayyukansu. Sai dai kamar yadda aka zata yanzu ’yan Boko Haram sun fara kai musu hari.
Shawara Okiro a biyo bayan wani hari ne da ‘’yan Boko Haram suka kai, bayan sun yi badda kama a cikin tufafin sojoji, ind asuka kashe jami’an saron matasa na sa kai har mutum 24, inda suka yi musu kwanton bauna a Munguno, kuma har yanzu ba a gano inda mutum 36 daga cikinsu suka shiga ba.
Babu ta yadda za a samu daidaiton karfi a tsakaninsu, kuma wannan hadari n da ya kamata a ce jami’an tsaro sun hango, sannan su gargadin matasan da su daina shiga wuraren da ke tattare da hadurra. Don haka a yunkurin warware wannan matsalar ba sai an bai wa matasan makamai da horon soja ba, domin su ma ’ya’ya n wadanda kamata ya yi a ce suna makaranta, ba a fagen yaki ba. Akwai wani hadarin da ke tattare da jefa matasa masu sa kai a harkar tsaro cikin yakin zubar da jinni a kokarinda ake yin a karya lagon Boko Haram, domin ’yan kungiyar matasan na iya juyewa su zama masu tayar da hankula. Tarihibn kafuwar ‘’yan Kalare a gombe da Sara-suka a Bauchi ko kungiyar kato da Gora ta Anambara da makamantansu, kamata ya yi su zama babban darasi ga Okiro da masu tunani irin nasa, cewa wannan kuskure ne, domin maganin fitina, a inganta wadanda aka horar don kawar ita. Shawara Mike Okiro tana da amtukar ban mamaki, ganin cewa akwai kwamitin da aka kafa a wannan yankin don shawo kan bazuwar kananan maikamai a Afirka taYamma, kuma akwai kwamitin shugaban kasa kan wannan al’amari.
Idan har matasa za su shiga cikin harkokin tsaro, abin da kawai suk bukata su ne na’urorin sadarwa, wadanda za su yi amfani da su wajen ankarar da jami’an tsaron JTF, don kawo daukin gagawa, ta hanyar amfani da kwarewarsu. Gwamnatin Jihar Barno ta yi abin da ya dace da ta samar wa ’yan kato da gora ababen hawa da kayan aiki, amma lallai an indaya iyaka kan ayyukan da ya kmata su yi. Idan aka samu wadanda suka nuna kwarewa, to a iya daukarsu aikin dan sanda, maimakon a rika biyansu alawus-alawus a kowane, ta yadda za su dogara da kansu.
A kasar da ake da karancin ’yan sandan da ke kula da al’umma, inda akalla dan sanda daya na kula da mutum dubu 10, tamkar yadda tsohon shugaban hukumar ’yan sanda, Mista Pary Osayande ya bayyana, cewa fiye a ’yan sanda dubu 10 daga cikin ddubu 330 na kasar nan an tura kula da wasu ’yan tsirarru mutane, inda suke dagon jakunkunan matan manyan mutanem wannan ba daidai ba ne. Amfani da ’yan sanda a matsayin amtaimaka na musamman ko masu gadi, ya zama alamar nuna matsayi a kasar nan, kamata ya yi a daina yin hakan. Abin takaicin ma shi ne wadannan jami’an akan yi amfani da su don cimma wani burin na son rai, wadanda suka hada da manufar siyasa ko huce haushi wasu mutane. Tsarin da sufeto janar na da , da mai ci a yanzu Muhammad Abubakar suka fito da shi na janye jami’an ’yan sanda daga ayyukan da ba su dace ba, har yanzu alkawuran kanzon kurege ne. Yanzu lokaci ya yi da za a aiwatar da aiki a aikace.
Dole ne hukumomi su fara shirin kula da matasan ’yan kato da gora don a amfana da su a gaba, tunda yakin ’yan tawaye ya kare. Tsare-tsaren gyaran kasa bayan kammala rikici ya kamata ya yi tanadi ga wkannan matsalar.