Mika Mulki: Buhari ya zagaya da Tinubu fadar shugaban kasa
Buhari ya zaga da Tinubu don nuna masa muhimman wurare da ke fadar shugaban kasa.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zagaya da zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban kasa ta Aso Rock da ke Abuja don don nuna masa muhimman wurare.
An gudanar da taron mika bayanan mulki gabanin bikin rantsar da shugaban kasa a ranar Litinin bayan da shugabannin biyu suka gudanar da Sallar Juma’a a masallacin gidan gwamnati.
- BIDIYO: Kalli yadda Jirgin Nigeria Air ya fara sauka a Abuja
- Sabuwar wakar Rarara ta sake yamutsa hazo
Babban jami’in hulda da jama’a na fadar shugaban kasa, Ambasada Lawal Kazaure, ya bayyana cewa jami’an fadar shugaban kasa da jami’an tsaro sun raka Buhari da Tinubu a yayin ziyarar.
A ranar Alhamis Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya yi nasa zagayen da zababben mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima a bangarensa da ke fadar shugaban kasa.
A farkon makon nan ne Aisha, matar Buhari, ta mika takardun ofishin uwargidan shugaban kasa ga matar Tinubun, Sanata Oluremi.
Tun da farko sai da ta dauki uwargidan shugaban kasa mai jiran gado zuwa ofishinta don nuna mata yadda wasu muhimman abubuwa suke.
A ranar Litinin ne za a rantsar da Tinubu a matsayin shugaban Najeriya na 16.