Mika ragamar Kaduna ga ’yan Kaduna

Tun zamanin da Turawan Ingilishi suka kafa garin Kaduna ake kiransa Garin Gwamna, har ya zuwa lokacin Sardauna Ahmadu Bello, ya zuwa kan gwamnonin da suka biyo baya, wadanda suka shimfida nasu salon mulkin iri daban-daban. Kowane Gwamnan yakan  bullo da wani al’amari, ko a ce wani aikin da yake so ya wanzar don daukaka […]

Mika ragamar Kaduna ga ’yan Kaduna
Mika ragamar Kaduna ga ’yan Kaduna

Tun zamanin da Turawan Ingilishi suka kafa garin Kaduna ake kiransa Garin Gwamna, har ya zuwa lokacin Sardauna Ahmadu Bello, ya zuwa kan gwamnonin da suka biyo baya, wadanda suka shimfida nasu salon mulkin iri daban-daban.
Kowane Gwamnan yakan  bullo da wani al’amari, ko a ce wani aikin da yake so ya wanzar don daukaka matsayin garin Kaduna wanda ya taba kasancewa hedkwatar Jihar Arewa, daya daga cikin jihohi ukun da ake da su kafin samun ’yancin kasar nan. Wannan jihar kuwa ita ce a halin yanzu aka tsintsinka ta gida goma sha tara.
Yawancin ayyukan da gwamnonin Jihar Kaduna suka aiwatar bayan wafatin Sa Ahmadu Bello ba su taka kara sun karya ba, hasali ma ba su canja kamannun jihar ba, kuma har ma  wadansu na yin ba’a game da haka: ‘wai da Sardauna Ahmadu zai  fito daga kabarinsa, ya kuma taka tiryan-tiryan  har  gidansa, to ba zai tsaya tambayar kowa ba, domin kuwa dukkan ababen da ya bari, hatta gidajen mutane da hanyoyin mota da gine-gine suna nan yadda ya mutu, ya bar su, babu wani canji ko  wata ’yar kwaskwarimar da aka yi musu.
 A takaice dai garin Kaduna, hedkwatar Jihar Kaduna, wacce ake wa kirari uwa-mai-bayar-da-mama, ya kasance koma bayan sauran hedkwatocin jihohin Arewa guda goma sha takwas da ya haifar, ya kuma rena.
Ko ba a fada ba, wannan babban abin takaici ne, domin kuwa  muhimmancin garin Kaduna a harkokin siyasa da na tattalin arzikin Arewacin kasar nan bai misaltuwa. A Kaduna ne ake yi wa dukkan al’amurran da  za a tsira ko gudanarwa a Arewa wankan tsarki. Shi ya sa ma ake cewa: ‘idan Kaduna ta yi atishawa, kasar gaba daya za ta tashi da mura.’ Ilai kuwa, Kaduna ta sha yin atishawa, kasar kuma ta sha kamuwa da murar da ta sha haifar mata da jente, sai an yi da gaske ake samun maganin warkarwa.
Malam Nasir el-Rufa’i, Gwamna na ashirin da daya  a Jihar, bayan wafatin Sardauna, ya fahimci haka, ya kuma sha alwashin maido da martabar jihar da ta kunshi wancan tsohon gari mai cikakken tarihi, abin alfaharin Sardauna. Haka nan dai ya sha fada tun lokacin yakin neman zabe a shekarar 2015, kuma koda Allah Ya tarfa wa garinsa nono, ya haye halifar Gamji dan kwarai, bai bar furta haka ba, yana nan kan bakarsa. Burinsa shi ne sake farfado da martabar garin Kaduna ala-kulli-halin, kuma ta kowace fuska, a dukkan fannonin ci gaba da raya kasa, kai ka ce da zarar ya gama rantsuwar zama Gwamna ba zai bata lokaci ba,  zai haye katafila ne, ya shiga aiki wurjanjan, ana farke tsofaffin hanyoyin da Sardauna ya yi da kansa don ingantawa; ana fadada hanyoyi masu matsatsi; ana sanya fitilu a dukkan tinunan unguwannin Kaduna; ana tono bututun famfon ruwa da suka yi tsatsa ana canjawa.
Amma ina! Haka nan awoyi suka dinga zamantowa kwanaki; kwanaki na zama makonni; makonni na zamewa watanni, kai har watannin suka cika na tsawon shekara guda cur, Nasiru bai hau katafila ba, martabar garin Kaduna kuma sai kara tabarbarewa take yi, ga kudi nan kuma yana ta tarawa tsagwagwa, amma ba wanda zai ce ga inda suke shigewa. In da kawai ya tura katafila da bulldozer shi ne makarantar Sakandaren Gwamnati ta Zariya, kuma sun bar harabar makarantar  jama’a na ta shirga  ihu da kururuwa, domin kuwa kasa ta gamu da kasa, gidajen wadansu sun kwanta dama, har ma wadansu masu gidajen an ce wai sun koma kwanciya a karkashin kasar. To wai me ya faru? Sun gamu da aikin Mai rusau.
Ko a Kaduna ma inda Sardauna ya  yi gine-gine masu armashi don kawata garin, Malam Nasiru sai da ya kukuta, ya yi rusau, ya bar dubun dubatan jama’a cikin bakar ukuba da rashin madafa, wadansu haka nan suka rika kwana a filin Allah Ta’ala, inda suke kwanciya rigingine, suna kirga taurari, kafin barci ya sace su. Wannan ba dabi’a ba ce ko hali irin na Sardauna, mai tausayawa da taimakawa. Kuma ko ba komai Malam Nasiru bai yi koyi da Sa Ahmadu ba a kokarinsa na daukaka matsayin garin Kaduna da kuma karrama mazauna cikinta, domin kuwa ya tsattsaga filaye bila-adadin a wurare da yawa, wadanda ya rarraba wa manyan ma’aikatan gwamnati da ’yan kasuwa, ’yan asalin Arewa,  sannan kuma daga bisani ya bullo da tsarin  tsarkake gwamnatinsa daga danniyar baki ’yan Kudu da suka mamaye dukkan ofisoshin gwamnati, bisa manya da kananan teburan gudanar da mulki. Wannan tsarin shi ake kira Mika ragamar jan Arewa ga ’yan Arewa. A lokacin ne ya yi bakin jini wajen ’yan Kudu, domin kuwa ya kakkabe ’yan uwansu da ke cin  gajiyar gwamnatin Arewa, ya maye gurbinsu da ainihin ’yan Arewa, wadanda suka ji dadin haka, suka kuma bayar da tasu cikakkiyar gudummawar da ta hanzarta kai Arewar ga kasaita da kuma yin kunnen doki da sa’o’inta.
A mamaikon haka, sai ga shi  yawancin jama’ar Jihar Kauna na kuka da Malam Nasir saboda ya mika ragamar Jihar Kaduna ga wadansu ’yan kalilan wadanda ba ’yan  asalin jihar ne ba, hakan kuma ya kawo cikas wajen gudanar da harkokin gwamnatinsa, ganin wadanda ya danka wa ragamar  su ne ke damawa a wadansu manyan ofisoshin gudanar da al’amuran gwamnati, su ne kuma suka yi derere bisa wasu mukaman da ba wanda ya isa ya ga Gwamna sai  ya bi ta kansu. Dangane da haka ne aka kasa gudanar da manyan ayyukan ciyar da jihar gaba domin wadanda za su mike tsaye, su tabbatar an yi, sun shantake, ganin cewa ba a jihohinsu ne za a yi aikin ba, suna can suna fafutikar dan abin da za su kankara ko su yayyaga, su aike da shi garuruwansu, a jihohin da  aka ce wai Malam Nasiru na burge jama’a, har yana yi musu hidindimu na fitar hankali,  wai don su cicciba shi kaiwa ga dandamalin takarar Shugaban kasa a shekarar 2019.
Babu wanda ke korafi game da takarar da Gwamna Nasiru zai so ya yi, idan har ya kintsa; amma abin da jama’a ke kuka da shi shi ne kin maido da hankalinsa ga jihar da yake ta fafa cewa zai farfado da martabarta, domin kuwa ya bari tana kara tabarbarewa, al’ummomin cikinta kuma na fita daga cikin kyakkyawan hayyaci.  Ai sai an gyara gida ne ake fita, a gyara daji, kuma idan gida bai koshi ba, kada a yi wauta ko gaggawar fitar da abinci zuwa wani gidan. Abin da ya kamaci Malam Nasiru aikatawa a halin yanzu, shi ne janye waccan ragamar da ya danka wa wadansu ’yan tsiraru daga Kudu, ya mayar da ita ga hannun ’yan Jihar Kaduna. Muddin ya yi haka to, su ma za su fi kowa agaza masa fitowa takarar shugabancin kasa da karfinsu, su  kuma sanya masa albarkar da za ta raka shi  har fadar Aso.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos