Mike Tyson ya ce kuskure ne Mayweather ya rika hada kansa da Muhammad Ali

Tsohon zakaran damben boding na duniya Mike Tyson da ake wa lakabi da “Iron Mike” ya ce babban kuskuren ne dan damben boding Floyd Mayweather ya rika hada kansa da shahararren dan damben boding na duniya da har yau ba a samu kamarsa ba Muhammad Ali. A makon da ya wuce ne Mayweather ya rika […]

Mike Tyson ya ce kuskure ne Mayweather ya rika hada kansa da Muhammad Ali
Mike Tyson ya ce kuskure ne Mayweather ya rika hada kansa da Muhammad Ali

Tsohon zakaran damben boding na duniya Mike Tyson da ake wa lakabi da “Iron Mike” ya ce babban kuskuren ne dan damben boding Floyd Mayweather ya rika hada kansa da shahararren dan damben boding na duniya da har yau ba a samu kamarsa ba Muhammad Ali.

A makon da ya wuce ne Mayweather ya rika hada kansa da Muhammad Ali bayan ya samu nasara a damben da suka yi da Packuaio.
“Na san wasu za su yi mini dariya, wasu kuma za su iya cewa na haukace idan na hada kaina da Muhammad Ali amma zancen gaskiya ni zan iya kwatanta kaina da Muhammad Ali ganin yadda na yi suna a duniya a fagen dambe kamar yadda Muhammad Ali ya yi suna”, inji Mayweather.
Jim kadan da wannan furuci ne sai dan damben ya fara samu suka daga bangarori da dama ciki har da Mike Tyson.
A damben da aka yi a tsakanin Mayweather da Packuaio, Mike Tyson ya goya wa Packuaio baya ne amma sai Mayweather ya samu nasara a damben.