Mike Tyson zai noma eka 40 na tabar wiwi a Amurka

Yayin da  sha  da kasuwancin tabar wiwi yake haramtacce a wasu kasashe, a Amurka  musammam  Jihar Kalifoniya, ba ma shan tabar ba, har nomanta ma bai haramta ba. Domin haka ne tsohon dan wasan danben  (boding) Mike Tyson ya share fili da ya yi girman eka 40 a Jihar Kalifoniya domin noma  tabar  wiwi. Gwamnatin […]

Mike Tyson zai noma eka 40 na tabar wiwi a Amurka

Yayin da  sha  da kasuwancin tabar wiwi yake haramtacce a wasu kasashe, a Amurka  musammam  Jihar Kalifoniya, ba ma shan tabar ba, har nomanta ma bai haramta ba.

Domin haka ne tsohon dan wasan danben  (boding) Mike Tyson ya share fili da ya yi girman eka 40 a Jihar Kalifoniya domin noma  tabar  wiwi.

Gwamnatin Jihar ta ce ta ba da damar noma tabar ce domin sarrafa ta a matsayin magani.

Sai dai kuma ba a hana shanta ba a zahiri ko kuma a nadata, kamar yadda ake  yi idan za a sha a boye a wasu wuraren na duniya.

Tyson dan shekara 51 da haihuwa zai noma wannann tabar ce a Jihar ta Kalifoniya a garin da ke da tazarar kilomita 110 daga birnin Los Angeles a wani wurin da ake kira Majabe Desert.

Wannan wurin kuma yana daf  da barikin Sojan sama da ake kira Edwards Air-Force Base.

Ya ce ya zabi wannan wurin ne domin ganin akwai inda tsoffin sojoji maza da mata suke zama domin za su bukaci tabar.

Sai kuma ya ce wannan tabar da zai noma za a rika amfani da sinadarin da ke cikin ganyen  domin sarrafa  maganin ciwon gajiya, haka kuma za a sarrafa wannan ganye ta hanyar kara  wasu sinadarai da za su samar da wasu magunguna daba-daban.

Yanzu  haka dai  daga cikin eka 40 da  zai noma, kashi 50  zai fara da shi sannan sauran kashi 50 zai yi amfani da shi ne wajen samar da sauran abubuwan da  masu aiki cikin gonar za su bukata tare da taimaka wa wani ko wasu da ke sha’awar yin irin wannan nomar.

Sannan kuma a cikin gonar za a samar da masana’antar sarrafa abinci na zamani da sauran ababen saukaka rayuwa da ke da nasaba da abinci.

Da yake yana da wadanda za su hada hannu da su kamar su Robert Hickman da Jay Strmmen  harma da magajin garin birnin Kalifoniya cikin wannan harka, wato Mayor Jenifer Wood kuma dukansu ’yan Kalifoniya ne.

Ya ce yana fatar ganin wannan ya kara kawo wa birnin na Kalifoniya karin  harkokin kasuwanci.

Wannan yunkurin da Tyson ya yi, yanzu wasu Amurkawa sun ce ba abin mamaki bane domin tun lokacin da yake dambe ya sha bayyana cewa fatarsa shi ne ya yi kasuwancin tabar wiwi, sannan kuma aka ce yana amfani da ita, wani lokacin ma ana zargin har da Cocaine yana shakawa.

Wannan yasa ko a danbensa na karshe a shekarar 2000 wanda ya yi nasara a karawar da suka yi Andrew Golota kuma Tyson din ya masa kaf daya, an jinkirta wannan nasarar domi an gwada shi kuma an tabbatar ya yi amfani da tabar ta wiwi kafin ya shiga danben.

Sai dai wannan yunkuri na Mike Tyson ya haifar da cec-kuce a ciki da wajen jihar.

Yayin da wasu ke kallon aikin da za a samu sakamakon samar da wannan gonar, wasu cewa  suke yi hakan zai kara lalala tarbiya da halin zamantakewar mutane musammam matasan da ke  wannan wurin domin a wasu  jihohn  shan wannan tabar  babban laifi ne.