Miliyoyin mutane sun yi shagalin kallon kusufin rana a Arewacin Amurka

Kusufin ya rufe sararin samaniya baki ɗaya tare da jefa birane a tsananin duhu har na tsawon mintuna.

Miliyoyin mutane sun yi shagalin kallon kusufin rana a Arewacin Amurka

Miliyoyin mutane ne suka yi dandazo a yankuna da dama na ƙasashen Arewacin Amurka don gane wa idanunsa yadda kusufin rana ya gudana, karon farko cikin shekaru 7 da yankin ke ganin wannan yanayi.

Cikin yanayin kada-kade da raye-raye baya ga yin mankas da barasa ne dandazon mutanen da suka ƙunshi matasa da kananan yara da kuma dattijai ne suka ganewa idonsu yadda kusufin na rana ko kuma dare biyu ya gudana a sassa daban-daban na ƙasashen Mexico da Amurka da kuma Canada, yanayin da ke zuwar wa yankin karon farko cikin shekaru bakwai.

An ga dai dandazon jama’ar wuraren shakatawar bakin ruwa na Mexico inda kusufin ranar ya faro zuwa gabar ruwan jihar Ohio na Amurka kana bakin ruwan Niagara da kusufin ya karkare, wanda ya shafe mintuna 3.5 zuwa 4 cikin duhu bakikkirin gabanin washewar gari.

Wannan ne karon farko cikin shekaru masu yawa da ƙasashen ke ganin irin wannan kusufi da ya rufe sararin samaniya baki ɗaya tare da jefa birane a tsananin duhu har na tsawon mintuna, dalilin da ya sanya mutane da dama yin balaguro zuwa sassan da za su fuskanci wannan kusufi tun gabanin zuwansa a jiyan don ganewa idonsu.

A Arkansas an ga yadda mutane dubu 30 suka fita kallon kusufin ranar yayin da wasu 400 suka yi amfani da damar wajen ɗaura aure mai cike da tarihi, can a Niagara kuwa da mutane dubu 2 suka fita kallon yadda aka ɗaura aure guda 2 da kuma baiko guda.

Mutane sun riƙa kuwwa cikin murna a lokacin da gari ya kammala dinkewa dif, yayin da aka saki waƙen R.E.M. na shekarar 1992 mai taken mutum akan wata.

Niagara kaɗai ya karɓi bakuncin mutane 309 daga Singapore da Landan waɗanda suka yi shiga sanye da wasu kaya masu tambarin rana don bikin kallon kusufin.

Tun bayan shekarar 2017 da yankin na Arewacin Amurka ya ga kusufin ranar ba a sake samun yanayin ba sai a yanzu, inda kuma hasashen masana ke cewa ba zai sake faruwa ba sai a shekarar 2044.