Miliyoyin ‘yan Tijjaniya za su halarci Mauludin Inyass gobe a Bauchi – Sheikh dahiru Bauchi

A gobe Asabar ne ake sa ran ’yan darikar Tijjaniya kimanin miliyan shida za su hallara a Bauchi domin halartar bikin Maulidin Sheikh Ibrahim Inyass na bana. Da yake zantawa da manema labarai a wajen taron makon Sheikh Inyass da aka gudanar a otel din Zaranda da ke garin Bauchi, fitaccen malamin Musuluncin nan Sheikh […]

Miliyoyin ‘yan Tijjaniya za su halarci Mauludin Inyass gobe a Bauchi – Sheikh dahiru Bauchi
Miliyoyin ‘yan Tijjaniya za su halarci Mauludin Inyass gobe a Bauchi – Sheikh dahiru Bauchi

A gobe Asabar ne ake sa ran ’yan darikar Tijjaniya kimanin miliyan shida za su hallara a Bauchi domin halartar bikin Maulidin Sheikh Ibrahim Inyass na bana.

Da yake zantawa da manema labarai a wajen taron makon Sheikh Inyass da aka gudanar a otel din Zaranda da ke garin Bauchi, fitaccen malamin Musuluncin nan Sheikh dahiru Usman Bauchi ya ce akwai baki daga kasashen Chadi da Nijar da Ghana da Senegal da Moroko da Aljeriya da dimbin mutanen da za su fito daga sassa daban-daban na duniya. Sheikh dahiru wanda ya ce za a gudanar da Mauludin ne a Dandalin Ibrahim Badamasi Babangida da ke Bauchi ya bukaci al’ummar birnin da na jihar su karrama bakin.
Daga cikin mutanen da suka halarci Makon Inyass din akwai Mai martaba Sarkin Dass Alhaji Bilyamu Usman wanda ya shawarci al’ummar Musulmi su hada kansu waje daya domin ciyar da addinin Musulunci gaba. Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da wakilin Sarkin Bauchi da na Gwamnan Jihar Malam Isa Yuguda.