Minista A`isha Jummai Alhassan: gaskiya ko kauyanci?

Tun ranar Larabar makon jiya da Hajiya A`isha Jummai Alhassan da a kan kira Maman Taraba, kuma Ministar Harkokin mata ta bayyana ra`ayinta kan cewa muddin tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana aniyarsa ta shiga neman takarar shugabancin kasar nan a shekarar 2019, ko da kuwa a wace jam`iyyar siyasa ce, to, […]

Minista A`isha Jummai Alhassan: gaskiya ko kauyanci?

Tun ranar Larabar makon jiya da Hajiya A`isha Jummai Alhassan da a kan kira Maman Taraba, kuma Ministar Harkokin mata ta bayyana ra`ayinta kan cewa muddin tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana aniyarsa ta shiga neman takarar shugabancin kasar nan a shekarar 2019, ko da kuwa a wace jam`iyyar siyasa ce, to, kuwa za ta ajiye mukaminta na minista ta kuma yi godiya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan nadata mukamin da yi, ta koma wajen tsohon mataimakin shugaban kasar, don ta mara masa baya, ta yadda zai kai ga nasara, ake ta ce-ce-ku-ce irin na siyasa, har wasu ma na cewa lallai sai Shugaba Buhari ya koreta.

Hajiya Jummai Alhassan ta fadi haka ne da sauran batutuwan siyasa, a wata hira da sashen Hausa na gidan Radiyon BBC, Landan, inda a cewarta, ita ba munafuka ba ce, tana mai jaddada cewa tsohon mataikamin shugaban kasar ubangidanta ne na siyasa, tun kafin ta shiga siyasa da bayan ta shiga. Kalaman na ta ko shakka babu suna zuwa ne a daidai lokacin da wasu jiga-jigan `yan siyasa da wasu magoya bayansu suke nuna ko kiraye-kiraye a kan na su gwanayen da su fito takarar neman shugabancin kasar nan, duk kuwa da sauran lokaci a kan zabubbukan 2019, din. 

Dadin dadawa bayyana ra`ayin Ministar harkokin matan, ba ya rasa nasaba da irin yadda su (magoya bayan Atiku) suke ganin Alhaji Atiku din a kullum yana kalaman da suke neman barrantarsa da jam`iyyarsa ta APC, mai mulki da gwamnatin tsakiya da uwa uba rashin lafiyar da Shugaba Buhari yake fama da ita a `yan watannin nan.

Hajiya Jummai, ta jaddada cewa, ko kusa ita ba munafuka ba ce, don haka da zarar Alhaji Atiku ya yanke shawarar zai tsaya takarar neman shugabancin kasa, to, ita kuwa za ta je ta durkusa gaban Baba Buhari ta ce da shi “ga mukaminka na gode.”

Ta kara da cewa kuwa da har yanzu Shugaba Buhari da Alhaji Atiku, ba su shaida wa kowa ba za su tsaya takara a zabubbukan shekarar 2019, in Allah Ya kaimu. A kan wadanda ta zarga da suna tura wa Shugaba Buhari sakonni ta wayoyinsu na hannu, suna fada masa wasu abubuwa da neman sai ya koreta, Ministar cewa ta yi Shugaba Buhari ba mahaukaci ba ne kamar masu tura masa sakonnin. Don haka ta san ba zai sauraresu ba, balle har ya koreta. 

“Har gobe ni `yar jam`iyyar APC ce, kuma ina aikina kamar yadda aka dora mani, ba a taba samuna da aikata wani laifi ba,” Inji  Hajiya A`isha Alhassan

Kamar sun hada baki, shi ma tsohon mataimakin shugaban kasar Alhaji Atiku, a dai ranar Larabar makon jiyan a wata hira da ya yi da sashen Hausa na gidan Radiyon muryar Amurka bOA, an ji shi yana fada wa duniya cewa an mayar da shi saniyar ware a cikin gwamnatinsu ta APC, ta yadda ba wata shawara da ake yi da shi, balle kuma neman ra`ayinsa duk kuwa da irin yadda ya ce su suka kama da sanayyarsu da kudin aljihunsu da karfinsu aka kafa gwamnatin.

Da ya ke tsokaci kan nasarorin da Gwamnatin Shugaba Buhari ta samu a kan yaki da cin hanci da rashawa, Alhaji Atiku ya nuna rashin gamsuwarsa a kan kasawar gwamnatin na ta hukunta barayin da ta kama balle kuma yawan kudaden da ta iya kwatowa, yana mai nuni da cewa a shigowarsu gwamnati a shekarar 1999, cikin karamin lokaci sun samu kwato Dalar Amurka biliyan 4.5 zuwa 4.7, daga wadanda suka sace su a zamanin mulkin Janar Sani Abacha. 

Akan yaki da masu tada kayar baya wato `yan kungiyar Boko Haram, tsohon mataimakin shugaban kasar ya yaba wa Shugaba Buhari a kan nasarar da ya samu, amma kuma ya ce ba ta kai ta a je a karas  ba, idan aka yi la`akari da yawan kananan hukumomi a jihohin Borno da Yobe da mutanensu suka kasa komawa garuruwansu da irin yadda har yanzu `yan kungiyar ta Boko Haram ke kashe mutane, da irin yadda ya bayyana mamakinsa a kan yadda aka kasa murkushe rikicin na Boko Haram, alhali wai an kawo karshe yakin Biyafara cikin watanni 30, yankin da ya ce yana da mummunan yanayin kasa da ya fi na shiyyar Arewa maso Gabas din.

Mai karatu ka iya cewa soke-soken gazawar gwamnatin ta Buhari da tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi soke-soke ne dan siyasar da ya rasa abin da zai ce don kawai ba a yi da shi, kamar yadda mataimakin shugaban kasar ya zargi Gwamnatin Buharin. Ai duk mai bibiyar yadda al`amurra suke tafiya a kasar nan ko ya karanta tarihi, ya san cewa yakin da aka yi da `yan kabilar Ibo, kwata-kwata ya sha bamban da na `yan kungiyar Boko Haram. Haka yaki da cin hanci da rashawar da su Atiku suka yi da wanda yanzu Buhari yake ko kusa ba iri daya ba ne a kan yanayi da yawan barnar da aka yi.

Daga irin yadda tsohon mai ba da shawara ga shugaban kasa  kan harkokin tsaron kasa, Kanar Sambo Dasuki (mai ritaya) da ake zargin ya raba Dalar Amurka $2.2biliyan kudin makamai ga jiga-jigan jam`iyyarsu ta PDP da sauran wadanda suke kauna da irin dimbin dukiya da kaddarori a ciki da wajen kasar nan da Hukamar EFCC, ta ce ta samu kwatowa ko tana kan binciken kwatowa daga tsohuwar Ministar man fetur Madam Deizane, kudaden da shugaban Hukumar ta EFCC Alhaji Ibrahim Magu ya ce wasa ne a kan kudaden da ake zargin tsohon shugaban kasa marigayi Janar Abacha ya sace. Ko kusa ba za ka hada su da na zamanin mulkin su Alhaji Atiku ba. Sai dai in ka sa siyasa

Bari mu dawo kan waccan hira da Maman Taraba, ta yi da sashen Hausa na BBC, inda har take cewa a cikin Ministocin Buharin akwai `yan jam`iyyar PDP, duk kuwa da ta ki bayyana sunayensu, wannan batu haka yake, don kuwa shi kanshi ubangidan na ta  Atiku Abubakar asalinsa dan jam`iyyar PDP ne, kuma duk da ya ce an mayar da shi saniyar ware a wannan gwamnatin ta APC, da ya ce sun ba da gagarumar gudummuwa an kafa, ai akwai makarrabansa da suka karbi mukamai a gwamnatin da sahalewarsa, na kuma tabbatar da cewa idan har ya yanke shawarar zai tsaya takarar neman shugabancin kasa mafi yawansu za su sauka daga kan mukamansu su dawo wajensa.

Mai karatu ka ga ke nan Maman Taraba, ko dai neman ta fadi gaskiya ko kauyanci ko ma rauni irin na `ya mace shi ya ja mata furta waccan magana. Mene ne ma sabo ai uwargidan Shugaba Buhari A`isha Buhari ita ma a bara ta shaida wa duniya cewar ba za ta mara wa maigidan ta ba ya ba a zaben 2019, muddin bai yi waje da wasu  da ta kira `yan shan kai a gwamnatin. 

Daga karshe sakona ga irin wadancan `yan siyasa, bai wuce su rinka sara suna duban bakin gatari, bisa ga irin yadda Allah ke nuna ikonSa wajen ba da mulkin ga wanda Ya so a lokacin da Ya so. Irin yadda Cif Obasanjo da marigayi Alhaji Umaru Musa `Yar`aduwa da Dokta Goodluck Jonathan suka hau kan karagar mulkin kasar nan cikin ruwan sanyi, sun ishi duk wani mai hankali ishara.