Minista daga Sakkwato: Buhari ya yi daidai
Zuwa ga Edita hakika Janar Buhari kana burgeni, saboda yadda kake dauko wadanda suka cancanta a mukamin minista, kamar a Jihar Sakkwato hakika saka Amina Abubakar a matsayin minista abu ne, wanda ya dace, duk wanda kake jin yana korafi a kanta yaran Alu Wamakko ne. Domin sun fi son komai sai su. To, idan […]
Zuwa ga Edita hakika Janar Buhari kana burgeni, saboda yadda kake dauko wadanda suka cancanta a mukamin minista, kamar a Jihar Sakkwato hakika saka Amina Abubakar a matsayin minista abu ne, wanda ya dace, duk wanda kake jin yana korafi a kanta yaran Alu Wamakko ne. Domin sun fi son komai sai su. To, idan ma Buhari ya saka wadda ba’a sani ba a matsayin minister, to mene ne laifinsa, tunda mun gani nan aka ce ga wanda ake son ya zama Shugaban Majalisar Dattawa, su Alu Wamakko suka yi tsaye da cewa sai Bukola Saraki. Don haka Buhari ya saka wadda yake ganin za ta yi wa talakawa aiki mene ne laifinsa? Saboda haka masu cewa Hajiya Amina Ta fito karamar hukama daya da Gwamnan Sakkwato, to Jihar Kebbi, wanda a ka saka sunansa a matsayin minista, Barista Abubakar Malami (SAN) karamar hukuma daya yake da Gwaman Kebbi Sanata Atiku Bagudu da kuma Shugaban Jam’iyyar APC na Jiha. Sun fito daga cikin garin Birnin Kebbi ne. Fatan mu kawai mu yi wa Buhari addu’ar Allah ya sa ya gama mulkin nan lafiya, ba cece-ku ce ba. Daga Usman Adamu Aliero Jihar Kebbi [email protected] 07061594299.