Minista: Dalilin Da Muka Ƙi Tantance El-Rufai —Kawu Sumaila
Sanata Kawu Sumaila ya yi tsokaci kan takaddamar sayar da filin jirgi na Malam Aminu Kano da shirin ECOWAS na yaki a Nijar
Sanatan Kano ta Kudu, Abdulrahman Kawu Sumaila, ya bayyana abin da ya hana majalisa tantance tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai domin zama minista.
Ya ƙara da cewa gwamnatin Shugaba Tinubu ta ji haushin yadda ’yan majalisa suka ki goyon bayan shirin Ƙungiyar ECOWAS na yaƙi da masu yi juyin mulki a kasar Nijar.
- Ministoci: Me ya sa Tinubu ya damƙa tsaro a hannun ’yan Arewa?
- Nijar: Za mu dawo da Bazoum ta kowace hanya —Sojojin ECOWAS
Kawsu Sumaila, wanda ya ce a shirye yake ya faɗi ainihin kuɗaɗen da ake biyan ’yan Majalisa, ya ce tallafin Naira 8,000 da gwamnati za ta bayar na cire tallafin mai yana da muhimmanci ga irin mutanen da gwamnatin take nufi.
Amma ya ce ya kamata gwamnatin ta dawo da tallafin man fetur bayan wata shida, idan har buƙata ba ta biya ba.
Ya kuma yi bayani kan taƙaddamar sayar da filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da kuma batun kuɗin hutunsu da ya jawo ce-ce-ku-ce.
Ga cikakken bidiyon tattaunawar da Aminiya ta yi da shi: