Minista ya caccaki El-Rufai kan sukar Tinubu da APC

Ministan ya ce babu abin da El-Rufai ya ƙware a kai face haddasa rikici.

Minista ya caccaki El-Rufai kan sukar Tinubu da APC

Ƙaramin Ministan Gidaje da Raya Birane, Yusuf Abdullahi Ata, ya caccaki Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, kan sukar jam’iyyar APC da kuma Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

A cikin wata sanarwa da hadiminsa, Seyi Olorunsola, ya fitar, ministan ya zargi El-Rufai da haddasa rikici saboda bai samu muƙamin minista ba.

Ya ce tsohon gwamnan mutum ne da ƙware wajen haddasa ce-ce-ku-ce da kuma yanke tsauraran hukunci a harkokin siyasa.

Ata ya ce lokacin da El-Rufai yake gwamnan Kaduna, an samu matsaloli da suka haɗa da rashin tsaro, rikicin ƙabilanci da addini.

Ya kuma ce komawar El-Rufai jam’iyyar SDP wata hanya ce da yake ƙoƙarin amfani da ita don a ci gaba da dama da shi a fagen siyasa.

Ministan ya yi watsi da iƙirarin El-Rufai na cewa Tinubu yana haddasa rikici a jam’iyyun adawa, inda ya ce wannan magana ba ta da tushe.

Ya jinjina wa Tinubu bisa jajircewarsa da ƙwarewarsa wajen bunƙasa siyasa, saɓanin El-Rufai da ya ce mutum ne da ke canza jam’iyya akai-akai don son zuciya.

Ata, ya tabbatarwa da ’yan Najeriya cewa APC na ƙoƙarin ci gaba da gina ƙasa, inda ya buƙace su da kada su saurari kalaman El-Rufai.

Ya ce gwamnatin Tinubu za ta ci gaba da aiki tuƙuru wajen bunƙasa tattalin arziƙi, bunƙasa ababen more rayuwa da tabbatar da tsaro.