Minista ya hori jami’an tsaro kan kare hakkin jama’a
Ministan tsaro Birgediya Janar Mansur dan Ali (mai ritaya), ya hori dakarun kasar nan, musamman wadanda ke aikin dawo da zaman lafiya a jihohin Yobe da Borno da Adamawa su zama masu kula da hakkin dan Adam a yayin gudanar da ayyukansu na tsaron kasa. Minista dan Ali ya bayyana haka ne yayin da ya […]
Ministan tsaro Birgediya Janar Mansur dan Ali (mai ritaya), ya hori dakarun kasar nan, musamman wadanda ke aikin dawo da zaman lafiya a jihohin Yobe da Borno da Adamawa su zama masu kula da hakkin dan Adam a yayin gudanar da ayyukansu na tsaron kasa.
Minista dan Ali ya bayyana haka ne yayin da ya kai ga Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Gaidam a ziyarar gani da ido da ya kai ga dakarun bataliya ta 3 da ke garin Damaturu a Jihar Yobe.
Ya ci gaba da cewa, lallai akwai bukatar jami’an soja su rika martaba al’ummomin da suka samu kansu cikinsu, ba wai su zame musu abin cutarwa ba. Ya ce ta yin haka ne za su rika samun hadin kai daga wajensu.
Ya tabbatar wa dakarun cewa, Gwamnatin Tarayya a shirye take ta ci gaba da samar musu da duk hakkokinsu, don ba su karfin gwiwar gudanar da ayyukansu. Ya ce yin hakan ne zai taimaka wajen samun nasararsu a fagen fama kamar yadda suke samu a kan ’yan ta’addar Boko Haram.
Ya kuma nemi Gwamnatin Jihar Yobe da kada ta gajiya wajen ci gaba da ba da goyon bayanta ga harkokin tsaro, domin hakan da gwamnatin ke yi ke kara karfafa gwiwar dakarun dangane yadda suke samun galaba a fafatawar da suke yi.
Da yake maida jawabi, Gwamnan Jihar, Alhaji Ibrahim Gaidam, ya yaba kan yadda sojojin ke gudanar da ayyukansu da irin nasarorin da suke samu a yakin da suke yi da ’yan tada kayar baya. Sai Gwamnan ya tabbatar wa ministan cewa, gwamnati da al’ummar jihar za su ci gaba da ba da goyon baya da hadin kai ga jami’an tsaron don ganin an kai ga nasarar wannan yaki.