Minista ya kaddamar da aikin samar da ruwan sha a Kazaure
A ranar Litinin da ta gabata ce Ministan Ruwa da Albarkatun kasa, Alhaji Suleiman Adamu Kazaure ya aza harsahin ginin cibiyar samar da ruwan sha a garin Kazaure da ke Jihar Jigawa, wadda ake sa ran kashe sama da Naira biliyan uku da miliyan 700. Minista Suleiman Kazaure ya fadi a lokacin da yake aza […]

A ranar Litinin da ta gabata ce Ministan Ruwa da Albarkatun kasa, Alhaji Suleiman Adamu Kazaure ya aza harsahin ginin cibiyar samar da ruwan sha a garin Kazaure da ke Jihar Jigawa, wadda ake sa ran kashe sama da Naira biliyan uku da miliyan 700.
Minista Suleiman Kazaure ya fadi a lokacin da yake aza harsashin gina cibiyar, cewa Gwamnatin Tarayya ta dauki matakin samar da ruwan sha a yankin ne domin amfanin al’umma da dabobi a kokarin gwamnatin na habaka harkokin rayuwar al’ummar kasar nan.
Ya ce “Ruwa shi ne ginshikin rayuwar dan Adam, lura da yadda gwamnatin Shugaba Muhammudu Buhari ta dauki amfanin gona da muhimmancin gaske.
Alhaji Suleman Adamu ya ce Gwamnatin Tarayya ba ta dauki harkokin samar da ruwan sha a matsayin al’amari mai sauki ba, ya ce inganta tsabtar muhalli da samar da ruwan sha shi ne mabudin rayuwar al’ummar kasar nan domin wata hanya ce ta bunkasar tattalin arziki a Najeriya.
Ya kara da cewar wannan ya nuna da gaske Gwamnatin Tarayya take yi wajen bai wa jama’a ruwan sha mai tsabta ta fuskar kara kudin kasafin bana a bangaren ruwan sha, inda aka samu fiffiko mai yawa a kasafin bana kan na bara, “Kuma wannan aikin na samar da ruwan shan da Gwamnatin Tarayya ta fara a Kazaure, an ba da shi ne kan za a kammala shi a cikin shekara daya. Sannan tuni Gwamnatin Tarayya ta amince Kamfanin CGC Nigeria Limited ya gudanar da aikin saboda nagartar aikinsa.
Ya ce “Gwamnatin Tarayya ta ware Naira biliyan 3 da miliyan 784 da dubu 885 domin yin wannan gagarumin aiki na samar da ruwa a Kazaure wanda ake sa ran kammala shi cikin wata 12.”