Minista ya kaddamar da amfani da na’urorin zamani a gidajen rediyo da talabijin
Ministan Watsa Labarai da Al’adu Alhaji Lai Mohammed ya kaddamar da sabon tsarin amfani da na’urorin zamani (digital) wajen watsa labarai a gidajen rediyo da talabijin a Najeriya a garin Jos babban birnin Jihar Filato a karshen makon jiya.Tsarin yana nufin masu sauraren rediyo da kallon talabijin wajibi ne su mallaki na’urar dikoda kafin su […]
Ministan Watsa Labarai da Al’adu Alhaji Lai Mohammed ya kaddamar da sabon tsarin amfani da na’urorin zamani (digital) wajen watsa labarai a gidajen rediyo da talabijin a Najeriya a garin Jos babban birnin Jihar Filato a karshen makon jiya.
Tsarin yana nufin masu sauraren rediyo da kallon talabijin wajibi ne su mallaki na’urar dikoda kafin su iya kallon talabijin ko sauraron rediyo a Najeriya.
Da yake jawabi a wajen bikin kaddamar da sabon shirin Minista Lai Mohammed ya
tabbatar wa ’yan Najeriya cewa duk wanda ya mallaki na’urar dikoda zai iya kallon dukkan tasoshin gidajen talabijin na Najeriya ba tare da biyan ko kwabo ba.
Ya ce za a raba wa mazauna garin Jos da kewaye akwatunan dikoda dubu 200 kyauta. Kuma ya ce sauran jihohi za su bi sahu, har a tabbatar tsarin ya karade kasar nan.
A jawabin Gwamnan Jihar Filato Barista Simon Lalong wanda Mataimakinsa Farfesa Sonni Tyoden ya wakilta ya mika godiyarsa ga Gwamnatin Tarayya kan yadda ta zabi Jihar Filato, a matsayin wurin kaddamar da fara wannan shiri a Najeriya.
Tunda farko a jawabin Darakta Janar ta Hukumar Kula da Tashoshin Rediyo da Talabijin ta Najeriya (NBC) Misis Alheri Sa’idu ta ce an fara wannan shiri ne tun a shekara ta 2006. Ta ce an
fuskanci matsaloli masu yawa kan shirin, amma tuni an riga an shawo kansu.
Shugabannin shirin sun ce akalla za a samar wa ’yan Najeriya sama da 2000 aikin yi wajen sanya akwatunan na’urori dikoda a sassan kasar nan.