Minista ya yaba wa ’yan jarida kan gudunmawarsu ga yaki da almundahana
Ministan Watsa Labarai Alhaji Lai Mohammed ya yaba wa ’yan jarida kan gudunmawar da suka bayarwa wajen yaki da cin hinci da rashawa a kasar nan. Alhaji Lai Mohammed ya bayyana haka ne yayin da yake marhabin da Shugaban Cibiyar ’Yan jarida ta Duniya (IPI) reshen Najeriya Alhaji Kabiru Yusuf ya jagoranci mambobin cibiyar suka […]
Ministan Watsa Labarai Alhaji Lai Mohammed ya yaba wa ’yan jarida kan gudunmawar da suka bayarwa wajen yaki da cin hinci da rashawa a kasar nan.
Alhaji Lai Mohammed ya bayyana haka ne yayin da yake marhabin da Shugaban Cibiyar ’Yan jarida ta Duniya (IPI) reshen Najeriya Alhaji Kabiru Yusuf ya jagoranci mambobin cibiyar suka kai masa ziyara a ofishinsa a Abuja.
Minista Lai Mohammed ya kara da cewa, “Ba muna nufin ku daina bin dokar aikinku ba ne, amma bai kamata a kasa daukar matsayi ba lokacin da ake neman ci zarafin Najeriya.” Alhaji Lai ya yi alkawarin kyautata jin dadi da kare hakkin ’yan jarida a Najeriya.
A jawabin Shugaban Cibiyar, Alhaji Kabiru Yusuf ya nanata bukatar cibiyar na ganin Gwamnatin Tarayya ta dauki nauyin taron ’yan jarida na duniya da za a gudanar a karkashin jagorancin cibiyar a shekarar 2018 , domin hakan zai ba da damar ganawa da manyan ’yan jarida na duniya tare da daukaka darajar kasar nan a idon duniya.
Alhaji Kabiru Yusuf ya ce cibiyar na shirin gudanar da taron horarwa ga ’yan jaridar Najeriya, musamman a bangaren kula da tsaron kansu ganin yadda harkar tsaro yake a Arewa maso Gabas da wasu sassan kasar nan.