Minista ya zabga wa wata mace mari a mashaya
Ana zargin Mataimakin Ministan Ilimi Mai Zurfi na Afirka ta Kudu Mista Mduduzi Manana da zabga wa wata mace mari lokacin da wata hayaniya ta barke a wata mashaya. Ministan dai har yanzu bai ce komai ba a kan batun. Sai dai a wata hira da aka nada, an ji wani mutum da aka yi […]
Ana zargin Mataimakin Ministan Ilimi Mai Zurfi na Afirka ta Kudu Mista Mduduzi Manana da zabga wa wata mace mari lokacin da wata hayaniya ta barke a wata mashaya.
Ministan dai har yanzu bai ce komai ba a kan batun. Sai dai a wata hira da aka nada, an ji wani mutum da aka yi amanna cewa Ministan ne yana cewa tabbas ya mari matar. Kuma gwamnatin kasar ta ce ba ta sane da zargin da ake yi wa Ministan.
Afirka ta Kudu tana daya daga cikin kasashen da ake yawan samun cin zarafin mata a duniya, inda alkaluman da ’yan sanda suka fitar suka nuna cewa an samu laifuffukan cin zarafin mata dubu 64 bara.
Wani mai magana da yawun ’yan sandan ya tabbatar wa Kamfanin Dillanci Labarai na AFP cewa suna bincike a kan lamarin da ya faru a ranar Lahadin da ta gabata.
Wani dan jaridar wata kafar labaran kasar, mai suna Lumko Jimlongo da ya gane wa idonsa abin da ya faru a mashayar Cubana da ke kusa da birnin Johannesburg, ya shaida wa kafar labarai ta Afirka ta Kudu (SABC) cewa, wadda aka mara ta yi kokarin ta fita a lokacin da ta gigice, amma “sai ta fadi a kasa, sannan kuma (Ministan) ya bi ta ya taka mata kai da kafarsa.”
Ministar Mata a Ofishin Shugaban Kasar, Susan Shabangu ta yi Allah wadai da zargin da ake yi wa Mataimakin Ministan. Kuma a wani bayani da ta yi ta kara da cewa, “ta yi matukar mamaki da takaici a lokacin da ta samu labarin.”
A wata hira da aka nada, mai dauke da maganganu a tsakanin dan uwan matar da Ministan, an tabbatar da mutumin da ya mare ta Minista ne saboda ta ce masa dan luwadi. Ya nuna cewa sauran mutanen da suke kusa da shi ne suka kara rura wutar rikicin.
Kafofin labaran kasar sun bayar da rahoton cewa, rikicin ya fara ne a kan an ce wa zai gaji Shugaba Jacob Zuma idan ya yi murabus, a matsayin shugaban Jam’iyyar ANC a watan Disamba mai zuwa.