Ministan Afirka ta Kudu da ya mari mace a mashaya ya yi murabus
Mataimakin Minsitan Ilimi Mai zurfi na kasar Afirk ta Kudu, Mista Mduduzi Manana ya yi murabus daga mukaminsa bayan da aka zarge shi da cin zarafin wata mace a wata mashaya a farkon watan nan. resigns ober assault claim Mista Mduduzi Manana dai ya bayyana a gaban kotu a makon jiya domin ya fuskanci tuhumar […]
Mataimakin Minsitan Ilimi Mai zurfi na kasar Afirk ta Kudu, Mista Mduduzi Manana ya yi murabus daga mukaminsa bayan da aka zarge shi da cin zarafin wata mace a wata mashaya a farkon watan nan.
resigns ober assault claim
Mista Mduduzi Manana dai ya bayyana a gaban kotu a makon jiya domin ya fuskanci tuhumar cin zarafai.
Ana zarginsa da marin wata mace ne a lokacin da suke musayar yawu a mashayar.
A ranar Asabar ce wata takaitacciyar sanarwa daga ofishin Shugaban kasar Jacob Zuma t ace, ya amince da murabus din Mista Manana inda ya gode masa kan “gudunmawar da ya bayar ga aikin gwamnati.’
Mista Manana ya nemi gafarar abin da ya kira “wani abin kunya.” Ya yi da’awar cewa an tunzura shi, “amma ya kamata a ce ya danne fushinsa,” inji shi.
Jam’iyyarsa ta ANC ta yi maraba da murabus dinsa, kuma ta yi masa godiya kan aikin da ya yi.
Lokacin da zargin ya bayyana ANC ta ce “Ba za a lamunci irin wannan hali ba… cin zarafin mata abin kunya ne a zamaninmu.’
Zargin ya jawo kakkausar suka a Afrika ta Kudu, wadda cin zarafin mata a cikinta ba bakon abu ba ne.
A yayin fara sauraren shari’arsa, an shigar das hi cikin kotu ne ta wata hkofa ta daban kuma aka hana ’yan jarida shiga ciki.
Sai dai Ministan ’Yan sanda Mista Fikile Mbalula ya nace cewa, Mista Manana ba zai samu wata kula ta musamman ba. “Ba za a nuna wa mataimakin ministan wata kula ta musamman ba, maimakon haka zai hadu da duk abin da doka ta tanada. kasar nana tana bayar da cikakken goyon baya ga wadda ya mara,” inji shi.
An bayar da belin Ministan a kan Dala 375 (kimanin Naira dubu 135), zuwa lokacin da za a kamala bincike.