Ministan da ya maye gurbin El-Rufai ya sume a wurin tantancewa

Majalisar Dattawa ta karbi bakuncin sabbin ministoci uku da Shugaba Bola Tinubu ya nada a zaurenta domin tantancewa

Ministan da ya maye gurbin El-Rufai ya sume a wurin tantancewa

Sabon ministan da Shugaban Tinubu ya nada daga Jihar Kaduna, Abbas Lawal Balarabe , ya sume a wurin tantance shi a zauran Majalisar Dattawa.

Abbas Lawal Balarabe, wanda ya maye gurbin tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai na daga cikin sabbin ministoci uku da suka je harabar majalisar domin tantancewa.

Jim kadan bayan majalisar ta tantance Ministar Matasa, Jamila Ibrahim Bio daga Jihar Kwara ne Abbas, ya hau kan mimbarin domin jawabin gabatar da kansa da kuma amsa tamboyin sanatoci, inda kimanin minti biyar bayan nan yanke jiki ya fadi.

Aminiya ta gano Abba ya fadi ne a daidai lokacin da Sanatan Kaduna ta Kaduna ta Kudu, Sunday Marshall Katung, yake tsokaci kan kwarewar ministan da irin ayyukan da ya yi a matsayin jimi’in gudarwa a Jihar Kaduna.

Sunday Marshal Katung ya sanar da amincewarsa da kuma ittifakin duk sanatocin Jihar Kaduna da nadin minista Balarabe.

Sanata Katung bai kai ga rufe baki ba ministan ya yanke jiki ya fadi, inda Shugaban Majalisar Godswill Akpabio ya yi kururuwa da cewa, “a taimaka masa da ruwa” ya umarci manema labarai su fice daga zauren, aka dakatar da tantancewar.

Aminiya ta gano ana ci gaba da kokarin farfado da Abba, kodayake wani sanata ya shaida wa wakilinmu cewa an farfado da shi.

Majalisar ta daura haramar tantance sabbin ministocin ne bayan kudurin da Shugaban Masu Rinjaye, Sanata Opeyemi Bamidele,  ya gabatar.

A ranar Talata Shugaba Tinubu ya gabatar da sunan Abbas Lawal Balarabe a matsayin minista daga Jihar Kaduna, wadda aka ware wa ma’aikatar muhalli.

Kafin nan, shugaban kasar ya mika wa majalisar sunan Jamila Bio Ibrahim daga Jihar Kwara a matsayin Ministar matasa, sannan Ayodele Olawande a matsayin karamin minista a ma’aikatar.