Ministan gona ya nuna damuwarsa a kan karancin madarar shanu a Najeriya

Ministan Al’amuran Nona Cif Audu Ogbe ya ce ana fuskantar karancin madarar shanu a Najeriya duk da cewar a Najeriya akwai shanu miliyan 19.5 amma duk da haka akwai bukatar a samar da karin shanu masu ba da madara domin ya wadata a Najeriya. A wani bikin nuna kayan amfanin gona da tattaunawa da masu […]

Ministan gona ya nuna damuwarsa a kan karancin madarar shanu a Najeriya

Audu Ogbe

Ministan Al’amuran Nona Cif Audu Ogbe ya ce ana fuskantar karancin madarar shanu a Najeriya duk da cewar a Najeriya akwai shanu miliyan 19.5 amma duk da haka akwai bukatar a samar da karin shanu masu ba da madara domin ya wadata a Najeriya.

A wani bikin nuna kayan amfanin gona da tattaunawa da masu ruwa da tsaki da aka yi tsakanin manoma da masu faba a ji a Jihar Jigawa,  ministoci hubu ne suka halarci wajen taron ciki har da Ministan Watsa Labarai Lai Muhammed da Ministan Harkokin Gona Cif Audu Ogbe da Ministan Albarkatun Ruwa Suleiman Adamu Kazaure da kuma Ministar harkokin mata.

Ya ce, kulawa da lafiyar dabobin zai taimaka wajen bunkasar madara da nama a fabin Najeriya haka kuma ba zai yiwuba dole sai gwamnati ta baiwa Fulani makiyaya kariya daga irin hare-haren da ake kaiwa Fulani makiyayan ana kashesu da dabobinsu.

Ya nuna takaicinsa game da yadda yara suke kashe iyayensu sakamakon bacin rai da mafiya yawan yaran suka sami kansu a ciki sakamakon kuncin rayuwa da suka sami kansu.

Ya kara da cewa, a duk rana a jahar Legas kabai ana yanka shanu dubu 7 a kullum kuma hakan baisa ansami karancin shanu a Najeriya ba duk da haka akwai bukatar gwamnati ta tashi tsaye wajan ganin an sami bunkasar karuwar shanu a fabin Najeriya duba da yadda rayukan dabobin suke salwanta.

Saboda haka akwai bukatar gwamnati ta mayar da hankali wajen kare rayuwar Fulani makiyaya da sukan su dabobin domin ganin an samar da madara da nama mai nagarta a fabin Najeriya.