Ministan ilimi ya bukaci ’yan Arewa mazauna Ribas su dabbaka koyarwar musulunci
Ministan kasa a Ma’aikatar Ilimi ta tarayya, Nyesom Wike, ya bukaci al’ummar Musulmi da ke zaune a Jihar Ribas da sudabbaka koyarwar addinin Musulunci, da ta hada da nuna kauna da zaman lafiya a tsakanin al’umma.Ministan ya yi bayanin ne a lokacin al’ummar Hausawa karkashin jagorancijn Alhaji Kampala Turaki suka kai masa a gidansa d […]
Ministan kasa a Ma’aikatar Ilimi ta tarayya, Nyesom Wike, ya bukaci al’ummar Musulmi da ke zaune a Jihar Ribas da sudabbaka koyarwar addinin Musulunci, da ta hada da nuna kauna da zaman lafiya a tsakanin al’umma.
Ministan ya yi bayanin ne a lokacin al’ummar Hausawa karkashin jagorancijn Alhaji Kampala Turaki suka kai masa a gidansa d ake Fatakwal. Sun kai ziyararnelokacin idin babbar sallah. Don haka ministan y ace addinin Musulunci addinin zaman lafiya ne, shi ya sa ya yi kira ga al’ummar Arewa da ke jihar da su yi zaman lumana da makwaftansu.
“Mafi aywanku a Jiahr Ribas aka haife ku kuma kun rayu a jihar tsawon shekaru. Muna son ku ci gaba da zaman lafiya, tare da bin dokokin kasa,” inji shi.
Y ace, gwamantin tarayya na aiki tukuru kwajen ganin ta shawo kan kunar bakin wake a Arewa. Bisa la’akari da nasarorin da soja suka wsamu, ina mai tabbatar muku da cewa, nan bad a dadewa ba, za a dawo da zaman lafiya da tsaro a yankin.