Ministan Kwadago ya zai fito takarar shugaban kasa

Ngige ya ce jam’iyyar adawa ma ta yarda cewa ya fi sauran masu neman kujerer shugaban kasa.

Ministan Kwadago ya zai fito takarar shugaban kasa

Ministan Kwadago, Chris Ngige

Ministan Kwadago, Sanata Chris Ngige, ya ce jam’iyyar PDP ta yi amanna cewa ya fi ’yan takararta da ke neman kujerar shugaban kasa a zaben 2023 nagarta.

Ngige wanda ya ce ba ya shakkan duk wani mai zawarcin kujerar ya bayyana haka ne a lokacin da yake sanar da shigarsa cikin jerin ’yan siyasar da ke neman takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023.

“Ba na tsoro ko shakkar komai, daidai nake da aikin, hatta ’yan uwanmu na jam’iyyar APGA za su shigo mu dunkule a tafi tare.

“Tafiyar ba ta APC kadai ba ce, ’yan uwanmu na PDP sun yarda cewa na zarce sauran masu neman mukamin a jam’iyyarsu idan ana batun tuntuba,” inji ministan, a  lokacin da yake bayyana aniyarsa a Jihar Enugu.

Ofishin yada labaransa ya bayyana cewa sai da Ngige ya tuntubi masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC mai mulki da babbar jam’iyyar hamayya ta PDP kafin cim ma wannan matsaya.

A ranar Talata, 19 ga Afrilu ake sa ran Ngige zai bayyana aniyarsa ta neman hakarar shugaban kasa a hukumance.

Ofishin ya ce Ngige ya bada dalilansa na tuntubar jam’iyyar hamayya da ya yi sa’ilin da yake jawabi ga magoya bayansa a garin Amansea bayan da ya ziyarci Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi na Jihar Enugu.

A cewar Ngige, “Na ziyarci Jihar Enugu ne a matsayin wani bangare na ci gaba da tuntuba, duk da dai shi (Gwamna Ugwuanyi) dan PDP ne, amma dai dan kabilar Ibo ne.

“Tsayayyen mutum ne shi, kuma kada a manta da cewa Enugu ita ce hedikwatar tsohon Lardin Gabas, sannan kun san mutunta juna abu ne mai kyau.

“Haka nan, na tuntubi wasu ’yan kasa wadanda ba ’yan kowace jam’iyya ba ne. Don haka na tuntubi Gwamnan Jihar Enugu game da aniyata ta takara don jin nasa ra’ayi dangane da haka. Saboda haka tafiyar ba ta APC kadai ba ce.”

Ya ce baya ga kasancewarsa tsohon Gwamnan Jihar Anambra, ya samu damar shiga cikin gwamnati kuma ya zama dan Majalisar Dattawa, don haka ya jaddada cewa, ya cancanci wannan aiki.

“Na shirya yi wa Najeriya aiki kwatankwacin yadda na yi wa Anambra,” in ji Ngige.

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna