Ministan Lafiya Ali Pate ya yi murabus
Minista a Ma’aikatar Lafiya Dokta Muhammad Ali Pate ya yi murabus daga gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan a shekaranjiya Laraba, inda ya ce, ya bauta wa kasar nan cikin mutunci, yayin da a zamaninsa a karon farko ba a samu bullar cutar poliyo mai nau’i ta uku ba cikin wata a fadin kasar nan.Wata sanarwa dauke […]

Minista a Ma’aikatar Lafiya Dokta Muhammad Ali Pate ya yi murabus daga gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan a shekaranjiya Laraba, inda ya ce, ya bauta wa kasar nan cikin mutunci, yayin da a zamaninsa a karon farko ba a samu bullar cutar poliyo mai nau’i ta uku ba cikin wata a fadin kasar nan.
Wata sanarwa dauke da sanya hannun mai taimaka wa tsohon Ministan Tashkalmah Hallah, ta cet Ministan ya yanke shawarar yin murabus ne bayan ya yi tuntuba sosai da kuma cikakkiyar kishin kasa da tawali’u.
Dokta Pate ya ce zai ci gaba da ba kasar nan goyon baya a matsayin mai bada shawara na musamman na girmamawa ga Shugaban kasa duk da ya karbi aikin Farfesa a Jami’ar Duke Unibersity’s Global Health Institute da ke Amurka, inda zai tsunduma wajen yi wa Afirka aiki da kuma zama babban mashawarcin Gidauniyar Bill and Melinda Gates Foundation da ke Washington, DC.
Da yake bayyana nasarorin da ya samu tun lokacin da aka kirawo shi daga Bankin Duniya a shekarar 2008, Dokta Pate ya ce, “un samu gagarumar ci gaba a ’yan wurare a bangaren kiwon lafiya a Najeriya: misali shirin ganin bayan cutar poliyo a karkashin shirin kula da kiwon lafiya daga tushe da aka amince da shi a shekarar 2010. Sai karuwar yawan wadanda suka kubuta daga cutar daga kashi 44 cikin 100 a shekarar 2008 zuwa kashi 90 a shekarar 2010 da sauransu.
Sai ya yi alkawarin tallafa wa shirin yaki da cutar poliyo na lokaci-lokaci a Najeriya da kuma shirin ceto rayuka miliyan daya.
Sai ya gode wa gwamnatin Najeriya kan ba shi damar yi wa kasar nan aiki, tare da bayar da tasa gudnumawa wajen bauta wa al’umma.