Ministan muhalli ya yi murabus daga mukaminsa

A yau Laraba karamin ministan muhalli Alhaji Ibrahim Jibrin ya mika takardarsa ta yin murabus ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin taron majalisar ministoci na mako-mako. Ministan ya ajiye aiki ne bayan da aka zabe shi a matsayin wanda za a nada ga mukamin sabon sarkin Nassarawa dake jihar Nasarawa. An nada ministan ne a […]

Ministan muhalli ya yi murabus daga mukaminsa

A yau Laraba karamin ministan muhalli Alhaji Ibrahim Jibrin ya mika takardarsa ta yin murabus ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin taron majalisar ministoci na mako-mako.

Ministan ya ajiye aiki ne bayan da aka zabe shi a matsayin wanda za a nada ga mukamin sabon sarkin Nassarawa dake jihar Nasarawa.

An nada ministan ne a watan Disamba ta 2015 bayan tantancewar majalisar zartarwa.