Ministan Noma: Manoma na jiran su gani a kasa

A ranar 15 ga Nuwamban shekarar 2015 Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta kaddamar da shirinta na bayar da lamuni ga manoman shinkafa a Jihar Kebbi. Ta yi haka ne a karkashin shirinta na ‘Anchor-Borrower’ na Babban Bankin Najeriya (CBN), don ganin ingantuwar noman shinkafa a kasar nan. Sannu a hankali, gwamnatin ta rika bin jiha bayan […]

Ministan Noma: Manoma na jiran su gani a kasa

A ranar 15 ga Nuwamban shekarar 2015 Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta kaddamar da shirinta na bayar da lamuni ga manoman shinkafa a Jihar Kebbi. Ta yi haka ne a karkashin shirinta na ‘Anchor-Borrower’ na Babban Bankin Najeriya (CBN), don ganin ingantuwar noman shinkafa a kasar nan.

Sannu a hankali, gwamnatin ta rika bin jiha bayan jiha tana bayar da lamuni ga manoman shinkafa na kasar nan. Al’amarin da ya kai ga zuwa yanzu, gwamnatin ta ba da shelar hana shigo da shinkafa kwata-kwata cikin kasar nan. Gwamnatin ta game kasa da ba manoman shinkafa wancan lamuni, lamunin da akasarin manoman suka yi kememe, suka ki biya, duk da cewa ta hanyar shugabannin Kungiyar Manoman Shinkafa ta Kasa (RIFAN) a jihohi Babban Bankin ya rika raba basussukan. Gwamnatin Tarayya ba ta daddara ba, har gobe tana ci gaba da raba basussukan noman shinkafa na biliyoyin Naira ga kungiyoyi manoman shinkafar. A yanzu ma ta kara da kungiyoyin manoman sauran cimaka, irin su masara da dawa, kai har da amfanin gonar da ba cimaka ba ne, irin su auduga.

Gwamnatin ta dage a kan ci gaba da raba irin wannan lamuni ne bisa ga wasu dalilai da suka hada da aniyarta ta farfado da ayyukan gona don samun dogaro da kai, a kan yadda kasar nan za ta iya ci da kanta da samar da ayyukan yi ga dimbin ’yan kasa, musamman matasa. Uwa uba da yadda za ta iya habaka tattalin arzikin kasar nan ta hanyar farfado da masana’antu masu dogaro da amfanin gona a zaman kayan sarrafawarsu da sauran dalilai.

Wadannan aikace-aikace na ganin bunkasar ayyukan gona na wannan gwamnati sun fara samuwa ne a karkashin jagorancin tsohon Ministan Ayyukan Gona da Raya Karkara, Cif Audu Ogbeh, wanda wadansu suka rika zargin ba kwararren manomi ba ne, wato ba ilimin ayyukan gona ya karanta ba, ko na tattalin arziki (yadda za a iya juya dari ya zama kwabo). Amma dai a kasar nan an san shi a matsayin babban manomin da har yakan ba da shawarwari ga gwamnatocin jihohi, kan yadda za su iya habaka ayyukan gona a jihohinsu. Ya taba shawartar Gwamnatin Jihar Borno irin wannan hikima ta noma. Dukkan nasarorin da za ka iya cewa a yau an samu ko za a samu nan gaba, sun ta’allaka ne kacokan a kan irin sha’awar da Shugaba Buhari da gwamnatinsa suke da ita wajen ganin lallai sai kasar nan ta zama mai dogaro da kanta, a kan samar da abinci da iya wadata masana’antunmu da kayayyakin sarrafawa, irin na amfanin gona da suke bukata.

A irin wannan hali, sabon Ministan Ayyukan Gona Alhaji Sabo Nanono ya karbi ragamar tafiyar da wannan babbar ma’aikata, mai matukar muhimmancin gaske. A duk kasar duniya da ta damu da zaman lafiyar mutanenta da habakar tattalin arzikinsu da ita kanta kasar, noma ne gaba. Shi din ma kamar Ministan da ya gada yake, wato babban manomi ne da kowa ya san shi a Jihar Kano. Bambancinsu kawai da Cif Ogbeh shi ne, shi masanin tattalin arziki kasa ne kuma tsohon babban ma’aikacin banki ne da ya san yadda za a rika juya dari ya zama kwabo ta hanyoyi da dama, ciki kuwa har da fannin ayyukan gona.

Kodayake babban labarin jan hankali a kan ayyukan gona da ’yan kasa suka fara ji daga bakin Minista Nanono, wanda kuma ya dage a kan gaskiyarsa, shi ne wanda ya yi a Abuja cikin watan Oktoban da ya gabata, a wajen bikin ranar Abinci ta Duniya ta bana. Ya ce “Da Naira 30 sai mutum ya ci ya koshi a Kano.” Wannan furici ya bude sabon babi a kan Ministan, wanda ya ja hankalin ’yan kasa da abokan aikinmu manema labarai da masu sharhi a kan al’amurran yau da kullum, inda aka yi ta furta albarkacin baki. Wadansu na cewa subutar baki ce, wadansu na cewa giyar mulki ce, wadansu na cewa watakila don Ministan manomi ne da ba ya yin awo. Wadansu kuma na cewa ko don dan boko ne da ya dade a kan mukami, ana ciyar da shi daga aljihun bankuna da hukumomin da ya shugabanta, don haka bai san tsadar abinci a yau ba.

A bisa ga ikon Allah a sanadiyar wani abu Allah Yake yin wani abu. Yanzu maganar da ake, wani mutum a cikin birnin Kano ya bude gidan sayar da abinci da ake biyan Naira 30 a ci abinci. Wannan dan talikin da bakinsa ya ce ana koshi daga irin nau’in abincin garin rogo da sukari ko da kuli-kuli da wake da shinkafa da mai da yaji da yake sayarwa. Mai gidan abincin, wanda ya tabbatar cewa zuwa yanzu wadansu sun kawo masa gudunmawar kusan Naira dubu 200 don tafiyar da sana’arsa. Daga cikin masu ba da gudunmawar har da ’yar Minista Nanono. Lokaci kawai zai tabbatar da dorewa ko akasin haka a kan wannan gidan abinci.

Bayan wancan furuci, an ji Minista Nanono a wasu jihohin kasar nan, inda ya kai ziyara yake kuma bayanin irin ayyukan da zai sa a gaba a zamansa na Ministan Ayyukan Gona. Alal misali a Jihar Kano, inda ya gana da kungiyoyin manoma daban-daban, Ministan ya tabbatar da cewa a zaman karfafa wa noman shinkafa da sarrafa ta, Gwamnatin Tarayya za ta kafa sababbin masana’antun sarrafa shinkafa 117, a dukkan fadin kasar nan, Kano kuma za ta samu 17.

Ministan kuma a wata ziyara da ayarin Hukumar Gudanarwar Kamfanin Buga Jaridun Daily Trust da Aminiya a karkashin jagorancin Malam Mannir Dan Ali suka kai masa a ofishinsa a makon jiya, ya sha alwashin ganin ya inganta wasu aikace-aikace guda uku, baya ga wadanda ya gada, don ganin ci gaban bunkasar ayyukan gona a kasar nan. Ayyukan uku sun hada da kara samar da malaman gona da kafa cibiyar da za ta rika tace amfanin gonar da aka yi aniyar fitarwa kasashen waje, don tabbatar da ingancinsu da kuma tsugunar da Fulani makiyaya.

Ya fadi cewa yana tunanin kafa wannan cibiya a babbar kasuwar hada-hadar amfanin gona mafi girma a Afirka ta Yamma da ke Dawanau kusa da Kano. Yayin da a kan tsugunnar da Fulani makiyaya kuma ya ce tuni ya kai ziyarar aiki a jihohin Bauchi da Gombe, inda ya duba wuraren da za a fara aikin tsugunnar da su, abin da ya ce zai kawo karshen fadace-fadacen Fulani makiyaya da manoma a kasar nan.

Ko shakka babu, manoma a kasar nan suna da kyakkyawan zaton samun ingantuwar ayyukan gona a wannan karo fiye da abin da aka yi a baya. Ina ga kuma ya kamata Minista ya tsaya tsayin daka wajen ganin an share dubba dazuzzukan da muke da su a sassan kasar nan don raba wa manoma. Kamar yadda shi ya sani, batun yau ba akwai matukar karancin gonaki. Bisa la’akari da irin yadda jama’ar kasa suka amsa kiran Gwamnatin Buhari na a koma gona da kuma irin tallafin da gwamnatin take badawa ga manoma daban-daban, yanzu kuma shi ne lokacin da ya kamata Minista Nanono ya dukufa a kai.