Ministan Sufuri ya jajanta wa al’ummar Gombe kan harin bam
Ministan Sufuri Alhaji Idris Abdullahi Umar ya kai ziyarar jajantawa ga al’ummar Jihar Gombe kan harin bam da ya auku ranar Juma’ar da ta wuce a tashar mota ta Gombe Line da ke Gombe. Ministan bayan ya zaga tashar motar da cibiyoyin lafiya da aka kwantar da wadanda suka ji rauni, ya ce ya ji […]
Ministan Sufuri Alhaji Idris Abdullahi Umar ya kai ziyarar jajantawa ga al’ummar Jihar Gombe kan harin bam da ya auku ranar Juma’ar da ta wuce a tashar mota ta Gombe Line da ke Gombe. Ministan bayan ya zaga tashar motar da cibiyoyin lafiya da aka kwantar da wadanda suka ji rauni, ya ce ya ji dadin ganin yadda likitoci suke kula da wadanda harin ya rutsa da su, inda ya yi addu’ar Allah Ya tona asirin wadanda suke aikata irin wannan ta’addanci. Ministan ya ce nan gaba zai kira taron kwamishinonin sufuri na kasar nan don ba da shawarar yadda za a kare tashohin mota daga kai hare-hare. Ministan ya bai wadanda harin ya shafa da ke asibiti tallafin Naira dubu hamsin-hamsin kuma ya bai sauran marasa lafiya da ke dakunan Naira dubu biyar-biyar. Shi kuwa Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Ibrahim dankwambo, kira ya yi ga jama’a su guji aiki da jita-jitar da ake yadawa cewa ’yan kabila kaza ne ko wane ne ya tada bam din don gudun barkewar rigimar kabilanci. Gwamna dankwambo, ya umurci likitoci su ci gaba da kula da marasa lafiyar, kuma ya ce gwamnati za ta daukin nauyin maganinsu, tare da tallafa wa iyalan wadanda suka rasu. Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Kudu Abdullahi Nma, ya ce sun kama mutum uku da suke zargi da tada bam din. Harin da ake zargin na kunar bakin wake ne da ya faru a ranar Juma’a da misalin karfe 9:15 na safe, ya kashe mutum 28 wasu 49 kuma suka samu raunuka, sannan motocin Gombe Line da na Kano 12 ne suka kone kurmus.