Ministan Tsaro ya jinjina wa Gwamnan Babagana Zulum na Jihar Borno

Ministan Tsaro, Janar Bashir Magashi ya jagoranci Babban Hafsan Sojin Kasa, Janar Yusuf Buratai da na Sama Abubakar Sadik da sauransu, don kai ziyara karfafa gwiwa ga dakarun da ke yaki da Boko Haram a Jihar Borno. Janar Magashi ya yaba  wa Gwamnan Jihar Babagana Umara Zulum kan yadda yake tunkarar kalubalen tsaron da ke […]

Ministan Tsaro ya jinjina wa Gwamnan Babagana Zulum na Jihar Borno
Ministan Tsaro ya jinjina wa Gwamnan Babagana Zulum na Jihar Borno

Ministan Tsaro, Janar Bashir Magashi ya jagoranci Babban Hafsan Sojin Kasa, Janar Yusuf Buratai da na Sama Abubakar Sadik da sauransu, don kai ziyara karfafa gwiwa ga dakarun da ke yaki da Boko Haram a Jihar Borno.

Janar Magashi ya yaba  wa Gwamnan Jihar Babagana Umara Zulum kan yadda yake tunkarar kalubalen tsaron da ke fuskantar jihar.

Ministan ya ce sun inganta fasalin yaki da rundunar tsaro ta kasashen yankin Tafkin Chadi kuma Gwamnatin Tarayya na kokarin bada kudade domin kawo karshen yakin na shekara 10 .

A jawabin Gwamna Babagana Zulum ya ce duk da kalubalen da ake fuskanta a yaki da Boko Haram, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya canja fasalin tsaro a jihar.

“A matsayina na Gwamna,  hakika Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi wa Jihar Borno komai, wajen taimakawa don ganin ta fita daga wannan bala’i na Boko Haram. Na san kokarin da Shugaban Kasa ke yi, duk da irin kalubalen da ake fuskanta, don haka muna gode masa. Sannan  kuma kai Ministan Tsaro da ka zo nan Jihar Borno sau 4 a cikin wata 6, ka cancanci yabo” inji shi.