Ministan tsaro ya umarci Buratai da ya koma Arewa maso Gabas
Ministan tsaro, Mansur Dan-Ali, ya umarci Hafsan Hafsoshin Sojojin Najeriya, Laftana-Janar Tukur Buratai , da ya ci gaba da zama a yankin Arewa maso Gabas don dakile hare-haren mayakan Boko Haram a yankunan. Hakan ya biyo bayan jawabin da Shugaban Najeriya ya yi akan inganta kayan aikin da sojojin Najeriya ke bukata musamman a wannan […]
Ministan tsaro, Mansur Dan-Ali, ya umarci Hafsan Hafsoshin Sojojin Najeriya, Laftana-Janar Tukur Buratai , da ya ci gaba da zama a yankin Arewa maso Gabas don dakile hare-haren mayakan Boko Haram a yankunan.
Hakan ya biyo bayan jawabin da Shugaban Najeriya ya yi akan inganta kayan aikin da sojojin Najeriya ke bukata musamman a wannan shirin da suke yin a dakile kai hare-hare a yankunan Arewa maso Gabas.