Ministan Wutar Lantarki ya yi murabus

Adelabu ya sanar da Shugaban Kasa Bola Tinubu, game da burinsa na tsayawa takarar gwamna a wata ganawa da suka yi a ranar Talata

Ministan Wutar Lantarki ya yi murabus

Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya yi murabus daga mukaminsa domin tsayawa takarar Gwamnan Jihar Oyo a shekarar 2027.

Hadiminsa, Bolaji Tunji, ya bayyana cewa Adelabu ya sanar da Shugaban Kasa Bola Tinubu, game da shirinsa na yin murabus da kuma burinsa na tsayawa takarar gwamna a wata ganawa da suka yi a ranar Talata.

Sanarwar ta ce,“Chief Adebayo Adelabu zai yi murabus daga mukaminsa a cikin ’yan kwanaki masu zuwa. Wannan mataki na nuna jajircewarsa wajen tabbatar da ci gaba da gyare-gyare a bangaren wutar lantarki kafin barin ofis.”

A cewarsa, ministan ya yi haka ne bayan da ya gabatar wa Shugaba Tinubu rahoton ayyukan da ya yi da kuma nasararoin da ya samu a lokacin da yake jagorantar ma’aikatar wutar lantarki a tsawon biyu da suka gabata.

Ya bayyana cewa ministan ya jinkirta ajiye aiki ne zuwa wannan lokaci domin ya samu damar kammala wasu muhimman ayyuka da tsare-tsare a bangaren wutar lantarki ta Najeriya.

A cewarsa, daga cikin muhimman abubuwan da ya gabatar akwai National Integrated Electricity Policy (NIEP) da Strategic Implementation Plan (SIP), wadanda za su zama jagora wajen ci gaba da samar da wutar lantarki mai dorewa a kasa.

Adelabu ya gode wa Shugaban Kasa bisa goyon baya da ya ba shi, tare da jaddada kudirinsa na ci gaba da bunkasa harkar wutar lantarki da ci gaban kasa baki daya.

Shugaba Tinubu ya yaba da kokarin Ministan, inda ya ce ya kafa tubalin manufofi masu karfi da za su sauya bangaren wutar lantarki.

Ya kuma amince da muradinsa na tsayawa takarar gwamna a Jihar Oyo.