Ministar Abuja ta raba motoci, babura da sauran kayayyaki ga mutum 4,064 a Kano

Ƙaramar Ministar Babban Birnin Tarayya Abuja, Dr Mariya Mahmoud Bunkure, a ranar Asabar ta kaddamar da shirin rabon kayan tallafi da kuɗaɗe ga mutun 4,064, a jihar Kano.

Ministar Abuja ta raba motoci, babura da sauran kayayyaki ga mutum 4,064 a Kano

Ƙaramar Ministar Babban Birnin Tarayya Abuja, Dr Mariya Mahmoud Bunkure, a ranar Asabar ta kaddamar da shirin rabon kayan tallafi da kuɗaɗe ga mutun 4,064, a jihar Kano.

Ta ce shirin, wanda galibin waɗanda suka amfana da shi mata ne da matasa, ya fito ne daga lalitarta ba daga asusun gwamnati ba, a matsayin wani bangare na aiwatar da manufofin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na inganta rayuwar ’yan Najeriya.

Mutanen da suka ci gajiyar tallafin sun samu motoci 6, babura 35, injinan murjin taliya 200 da fulawa, injinan nika 200, buhunan taki 400, buhunan shinkafa 1,000, kekunan guragu 30, keken ɗinki 200, tare da tallafin kuɗi na Naira 30,000 ga mutum 2,000.

A wajen taron, Dr Mariya ta ce shirin ba wai rabon tallafi kawai ba ne, wani yunkuri ne na sauke nauyin da ke wuyansu tare da tabbatar da babu ɗan Kanon da aka bari a baya.”

Ta kuma yaba wa mata da matasa bisa rawar da suke takawa wajen ƙarfafa jam’iyya, tana mai cewa idan mata sun tsaya da ƙarfi, al’umma kan bunƙasa.

Ministar ta kuma bayar da albishir cewa wannan shirin somin-taɓi ne, akwai wasu da yawa na nan tafe.

Ita ma da take nata jawabin, Ƙaramar Ministar Ilimi, Suwaiba Sa’id Ahmad, ta ce bunƙasa rayuwar ɗan adam na kan gaba a cikin manufofin gwamnatin tarayya.

Ta kuma ce ma’aikatar ilimi ta kuduri aniyar talkafa wa ’yan Najeriya 250,000, inda tuni suka fara da mutum 100,000 a rukuni na farko.

Ita ma matar tsohon Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Hafsat Abdullahi Ganduje, ta yaba wa ministar bisa wannan ƙoƙarin, tana mai cewa jamiyyar APC ba ta da burin da ya wuce na inganta rayuwar ’yan Najeriya.