Ministar kudi ta yi kaca-kaca da tsohon Gwamnan Babban Banki

Ministar Kudi Misis Ngozi Okonjo-Iweala ta ragargaji tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Farfesa Chukwuma Saludo bayan da ya soki yadda Shugaba Goodluck Jonathan ke tafiyar da tattalin arzikin kasar nan, inda ta ce bayaninsa “soki burutsu ne.” Ministar wadda ta yi magana ta bakin kakakinta, Paul Nwabuikwu, ta zargi Farfesa Soludo kan yadda ya […]

Ministar kudi ta yi kaca-kaca da tsohon Gwamnan Babban Banki
Ministar kudi ta yi kaca-kaca da tsohon Gwamnan Babban Banki

Ministar Kudi Misis Ngozi Okonjo-Iweala ta ragargaji tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Farfesa Chukwuma Saludo bayan da ya soki yadda Shugaba Goodluck Jonathan ke tafiyar da tattalin arzikin kasar nan, inda ta ce bayaninsa “soki burutsu ne.”

Ministar wadda ta yi magana ta bakin kakakinta, Paul Nwabuikwu, ta zargi Farfesa Soludo kan yadda ya rika tafiyar da harkokin aikin banki shi kadai daga watan Mayun shekarar 2004 zuwa Mayun 2009 tare da jefa kasar nan a cikin yanayi na “gagarumar asarar da za ta ci dukiyar ’yan Najeriya Naira tiriliyan biyar da biliyan 670,” inji ta.
Misis Okonjo-Iweal ta bayyana tsohon Gwamnan Babban Bankin da “mutumin da yake fama shan kaye a fagen siyasa,” wanda “ruwa ya ci” kuma “ya rasa alkibla yana murguda bayanai kan tattalin arziki da gangan kuma yake kawo wasu kididdiga na karya domin rikita ’yan tunanin Najeriya don cimma wata manufa tasa,” inji shi.
Misis Okonjo-Iweala ta ce, “Ba kunya Soludo ya rika kawalci ga wasu tsofaffin shugabanni cewa ’yan Najeriya suna bukatarsu su kara wa’adi – wane mukami Soludo yake nema a yanzu?” ta yi tambaya.
Ta ce, “Hakika akwai matsalar dabi’a a tare da Farfesa Soludo. Charles Soludo na da mugun kwadayin mulki da son tagomashi, akwai bukatar ’yan Najeriya su rika lura da masu kiran kansu masana amma ba su da kyakkyawar dabi’a da hikima, domin rasa wadannan abubuwa biyu hadari ne.”