Ministar Mata Ta Hana Shugaban Majalisar Neja Aurar Da Marayu 100
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Neja, Barista Abdulmalik Sarkindaji, ya janye aniyarsa ta aurar da marayu 100 a mazabarsa. Shugaban majalisar ya fasa aurar da marayun ne bayan ministar harkokin mata, Uju Kennedy-Ohanenye, ta nuna damuwa da game da ko an tabbatar da amincewar ’yan matan da shekarunsu, kamar yadda doka ta ayyana. Sarkindaji ya bayyana […]
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Neja, Barista Abdulmalik Sarkindaji, ya janye aniyarsa ta aurar da marayu 100 a mazabarsa.
Shugaban majalisar ya fasa aurar da marayun ne bayan ministar harkokin mata, Uju Kennedy-Ohanenye, ta nuna damuwa da game da ko an tabbatar da amincewar ’yan matan da shekarunsu, kamar yadda doka ta ayyana.
Sarkindaji ya bayyana wa manema labarai hakan ne a harabar majalisar a ranar Talata, inda a cewarsa ya gama shirye-shiryen daurin auren, har ya biya kudin sadaki a madadin angwaye.
Sarkindaji ya ce ya bar wa shugabannin gargajiya da na addinin yankin amanar daurin auren, ya ba su dama su yanke hukunci kan batun, amma shi ya hakura tun da abin ya janyo ce-ce-ku-ce.
- Matsahi ya cinna wa mutane wuta suna sallar Asuba a masallaci a Kano
- JAMB ta sake fitar da sakamakon ɗalibai 36,540
Honaabul Barista Abdulmalik Sarkindaji ya bayyana rashin jin dadinsa da matakin na ministan mata ta Najeriya, ya ce bai tilastawa ‘yan mata auren ba.
Ya ce iyayen yaran ne suka tuntube shi don neman tallafi, ya kuma yanke shawarar daukar nauyin auren ne bayan ya tuntubi malaman addini da shugabannin gargajiya, da sauran masu abin cewa kan harkokin jama a kafin ya amicne.
Shugaban majalisar ya sa an zabo mata 100 daga cikin 270 da ke son aure amma babu hali.
Ya kuma caccaki ministar kan yadda ta rika yada batun a kafafen sada zumunta ba tare da ta tuntube shi domin sanin gaskiyar lamarin ba.
Ya bukaci ta ziyarci sansanonin ’yan gudun hijira a jihar Neja domin fahimtar kalubalen da ’yan matan da iyayensu ke ciki.